Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana ya bayyana cewa an saki matasan da aka kama yau cike makil a motan daukan kaya tare da baburan su a kusa da garin Ikko, jihar Legas.
‘yan sandan jihar Legas sun kama wani motan kaya cike makil da matasa 123 da baburansu 48 zasu shiga garin Legas a yammacin Asabar.
ElKana ya ce bayan an gudanar da bincike sai aka gano ashe ‘yan cirani ne dake balaguro da harkar neman abinci a garin Legas.
” Mun gano cewa ashe ‘yan cirani ne da ke zuwa jihar Legas domin yin sana’o’i. Kuma dukkan su ‘yan asalin jihar Jigawa ne. Wasunsu ma suna da iyalan su a Legas ne wasu kuma ma sun dade da zama a jihar sun tafi duba gida ne.
” A dalilin haka bayan muntantance su sai muka tabbatar ba muggan iri bane sai muka sake su kowa ya je ya ci gaba da sana’arsa.
Wani mazaunin jihar Kaduna da yake tofa albarkacin bakinsa game da wannan abu da ya faru ya ce duk da an sake su yadda suka taru a mota daya haka a cunkshe kamar dabbobi bai dace ba.
” Irin wannan tafiya da ‘yan Arewa suke yi ya kan tozarta yankin. Ace matasa majiya karfi irin wadannan da aka kama su cunkushe a cikin mota haka da babura wai zasu aikin acaba ai bai dace ba. hakan na ssa ayi wa ‘yan Arewa cin mutunci da fuska matuka.” Inji Hassan Sani.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=1TQDKHYQDMw&w=560&h=315]
Discussion about this post