‘Yan sanda sun kama dillalan makamai dauke da harsasai 10,000

0

Jami’an ‘yan sandan Jihar Oyo sun bada sanarwar kama wasu rikakkun masu safarar muggan makamai.

An hakkake cewa su na sayar da su ne da wasu gungun masu aikata fashi da makami a cikin Ibadan da kewaye.

Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Oyo, Sina Olukolu ya gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai a yau Alhamis, a hedikwatar su da ke Eleyele, cikin Ibadan.

Ya ce an same su dauke da harsasai har 10,000. An kama su ne bayan da rundunar SARS su ka ji labarin wata mabuyar su a unguwar Oke Bola cikin Ibadan.

“Wadanda aka kama din sun hada da Adekunle Abimbola, Abel Kojo, Mukaila Ariyo da Ade Adebayo.

“An samu harsasai dubu goma a hannun su, kuma an kama su tare da mota kirar Toyota Sienna LE, wadda ba ta da takardu ballantana lamba. An kuma samu Toyota Cmary mai lambar Lagos GGE 979 FT a hannun su.”

Daya daga cikin wadanda aka kama da harsasan mai suna Abel Kojo, ya ce a gaskiya ba shi da lasisin sayar da makamai, amma shi dai niyyar sa ita ce ya sayar da harsasan ga mafarauta tsuntsaye da namun daji.

Ya kara da cewa sama shekara daya kenan ya na sana’ar sayar da harsasan bindiga.

Kwamishinan ‘yan sanda ya gargadi jama’a su rika sa ido sosai domin akwai mugaye wadanda ke cudanya cikin mutane nagari.

Kuma ya ce a kara sa-ido, musamman a wannan lokaci da bukukuwan sallah ke karatowa.

Share.

game da Author