‘Yan sanda sun ceto daliban jami’ar Ahmadu Bello da aka yi garkuwa dasu a titin Abuja-Kaduna

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa a yammacin Laraba, zaratan ‘yan sanda na (IRT) da wasu zaratan dake aikin fafurar masu garkuwa da mutane sun ceto daliban jami’ar Ahmadu Bello da aka yi garkuwa da su a a Titin Kaduna-Abuja.

Sabo yace bayan samun labarin aikata wannan mummunar aiki da masu garkuwan suka yi ne sai ‘yan sanda suka fantsama cikin dajin domin kamo wadannan bata garai.

” Allah ya bamu sa’an ceto dalibai uku da aka yi garkuwa da su sannan sauran ukun cikin mutane shida da aka tafi da su har yanzu suna tare da masu garkuwan amma kuma zaratan mu suna nan suna farautar su.

Sabo ya kara da cewa wadannan masu garkuwa sun bude wa motan fasinja wuta ne suna sanye da kayan sojoji don badda kama kuma ya ce har yanzu jami’a na can cikin daji suna farautar masu garkuwan da kuma kokarin ceto sauran da ke tsare a hannun su.

Idan ba a manta ba ko a ranar Laraba ma an rika yada wani bidiyo da ke nuna yadda masu garkuwan suka tare wannan titi suka yi garkuwa da mutane.

A wannan bidiyo ance saida tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya tukari wannan wuri tareda masu tsaron sa sannan masu garkuwan suka arce cikin daji.

Share.

game da Author