‘Yan sanda na neman inda aka yi garkuwa da mai caccakar Ganduje

0

Jiya Asabar ne Rundunar ‘Yan sandan Kaduna suka fara neman yadda za su kubatar da Abubakar Idris, wani wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

An yi garkuwa da Idris ne wanda aka fi sani da suna Dadiyata bayan da aka yi masa takakkiya har gida a Kaduna a ranar Alhamis, aka yi awon gaba da shi.

Iyalan sa sun shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Jima’a cewa an arce da shi ne a daidai lokacin da ya ke kokarin shiga cikin gida da motar sa a Barnawa, wajen karfe 1: na rana.

Duk da cewa dai ba a san inda Dadiyata ya ke ba, amma wata majiya daga cikin iyalan sa, sun ce jami’an SSS ne suka yi awon-gaba da shi.

Wasu makusantan sa ma sun ce an ga daidai lokacin da jami’an SSS ke kokarin tura shi cikin ofishin su a Kaduna.

PREMIUM TIMES dai ba ta tabbatar da shin SSS ne suka kama shi ba, ko kuwa garkuwa ce aka yi da shi. Amma dai SSS sun ki amsa tambayoyin da wannan jarida ta aika musu domin sanin ko su ne suka kama Dadiyata, wanda ya yi suna sosai wajen sukar Ganduje.

A na su bangaren, ‘yan sandan Kaduna sun ce sun samu cikakken bayanin yadda aka tafi da sh, kuma su na kokarin ganin ya koma cikin iyalin sa lafiya.

An yi cacukui da Dadiyata ne bayan da ya riga ya shiga da motar sa a cikin gidan sa. Sai wasu mutane biyu dauke da bindigogi suka rufar masa, suka gudu da shi a cikin motar sa kirar BMW.

Jami’an tsaro sun shaida cewa Dadiyata malami ne da ke koyarwa a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma, Jihar Katsina. An san shi sosai wajen ficen da ya yi ya na sukar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a soshiyal midiyal midiya.

Wannan ya sa Dadiyata wayan yin sa-in-sa na kakkausan martanonin rubuce-rubuce tsakanin sa da hadiman Ganduje a soshiyal midiya.

Share.

game da Author