Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a cikin watanni bakwai ‘yan bindiga sun kai hare-hare har sau 330, tare da kashe adadin mutane 1,400, daga Janairu zuwa Yuli.
Babbar Sakatariyar Kula da Ayyuka na Musamman a Ofishin Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Amina Shamaki ce ta bayyana haka, a yayin taron da ake kan gudanarwa a kan matsalar tsaro, a Jihar Kebbi.
Amma kuma Babbar Sakatariyar ta ce a yanzu hare-haren sun fara raguwa matuka.
Ta ce Shiyya Arewa maso Yamma da aka sani da zaman lafiya, a shekarun baya ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Shamaki ta kara bayanin cewa har yanzu matsalar tsaro a shiyya abin damuwa ce kwarai ainun ga jami’an tsaro da sauran al’umma baki daya.
Ta kuma yin nuni da cewa raguwar kashe-kashen da aka samu, sun faru ne saboda matakan da aka dauka a jihar Zamfara.
“Zaman sasantawar da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle musamman, da kuma wasu gwamnoni suka kirkiro, ya zama abin yabawa matuka. Don haka ana fatan sauran jihohi masu irin wannan matsala su dauki irin darasi daga gare su, domin shawo kan matsalar su.
“Matakin a-ciza-a-hura da ake dauka domin kawo karshen wannan fitina, abu ne mai muhimmanci, tunda an fara ganin biyan bukata a wasu yankuna.
Har ila yau ta kuma nuna damuwa dangane da wata gagarimar matsalar shigo da mugga da kananan makamai da ake yi a kasar nan, daga kasar Libya, wadda yaki ya ragargaza.
A karshe ta yi kira ga shugabanni da mazauna yankunan da suka yi makwautaka da wasu kasashe da su rika wayar da kan al’umma tare da gargadin su a kan illar bai wa bakin-hauren da ba su san asalin su ba mafaka ko wurin zama.