‘Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah

0

An bindige Mataimakin Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya da aka fi sani da Miyetti Allah na shiyyar Yankin jihar Adamawa ta Kudu.

An bindige Saidu Kolaku ne jiya Asabar, kuma wani daga cikin jami’an kungiyar da ma wasu daga cikin jihar sun tabbatar da cewa kisan daukkar fansa ne.

Kolaku ya kokari sosai wajen taimaka wa jami’an tsaro wajen gano mabuyar masu garkuwa da mutane da sauran masu fashi da manyan laifuka.

Kwanan nan ne ma Hukumar ’Yan Sanda ta Jihar Adamawa ta karrama shi bisa irin kokarin da ya ke yi wajen magance matsalar tsaro.

Shi ma Kakakin Yada Labarai na Rundunar, Suleiman Nguroje ya tabbatar da kisan da aka yi wa Kolaku.

‘Wasu ’yan bindiga da ba a kai ga gano ko su wa ba ne, sun bindige daya daga ckin shugabannin kungiyar Miyetti Alah. Sun je har gida suka yi masa takakkiya garin Sabon Pegi cikin Karamar Hukumar Mayo Belwa, suka harbe shi suka bar shi a cikin jini.

Ya kara da cewa an yi wa jami’an tsaro kiran gaggawa bayan an yi kisan, kuma suka je suka samne shi babu rai.

Ya ce a na nan ana zurfafa binciken makasan kuma za a gano su duk inda suka buya.

Ngoruje ya nuna bakin cikin rashin Kolaku da aka yi, musamman a wannan mawuyacin hali da ya ke a kan ganiyar ganin an kakkabe makasa da sauran manyan masu fashi.

Da ya ke magana, Kakakin Yada Labarai na Miyetti Allah a Jihar Adamawa, Muhammad Buba, ya ce kisan sa zai iya kasancewa daukar fansa ce wasu mahara suka yi, saboda rawar da ya taka sosai wajen dakile masu fashi da garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.

“Idan ba a manta ba, an karrama Kolaku ne a ranar 17 Gayuli, 2019, saboda namijin kokarin da ya ke yi wajen taimaka wa jami’an tsaro ana kama mahara, masu shatar shanu da fshi da makami.”

Buba ya nuna takaicin rashin Kolaku a wannan hali da ake bukatar sa da sauran ire-iren sa a cikin al’umma.

Share.

game da Author