Tsohon Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Bankado Kayan Sata, Okoi Obono-Obla, ya yi abin nan da Hausawa ke cewa ‘wanzami ba ya son jarfa, inda ya garzaya kotu ya kalubalanci binciken sa da ICPC ke yi.
Obla ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta bada labara cewa ICPC ba ta da hurumin bincikar sa a kan zargin mallakar satifiket na bogi.
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Obla daga shugabancin hukumar bankadowa da kwato kayan sata, har zuba bayan kammala binciken da ICPC ke yi,
A cikin takardar dakatarwar da aka damka masa, wadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya sa wa hannu, an nuna cewa “zai ci gaba da zama a dakace, har sai kwamitin bincike ya kammala aikin sa tukunna. Saboda akwai kuma zargin baddala alkaluman kididdigar kudade da walle-wallen kudade da ake zargin ka yi.”
Ana sa ran Obla ya mika kan sa ga Hukumar ICPC domin a bincike shi, biyo bayan zargin fojare da ake yi masa.
Obla, wanda ya yi digiri na shari’a da aikin lauya a Jami’ar Jos, mamba ne na Kungiyar Lauyoyin Najeriya, NBA. Ana zargin sa da shiga jami’a ne da takardun jabu na karya.
Shi kuma ya ce karya ce da sharri wasu ke masa, saboda bankado satar da ya rika yi sun tabka.
A karar da ya shigar kotu, ya ce ICPC ba ta da hurumin gayyatar sa, damke shi, kulle shi, binciken sa ko gurfanar da shi a kotu dangane da zargin mallakar satifiket na jabu.
Da ya ke nuna korafin dakatar da shi da aka yi, Obla ya shaida wa kotu cewa ai shi ma ya sha binciken manya da dama wadanda ake zargi da wawurar kudade, kuma duk da suna kam mukaman su, ba a dakatar da su a lokacin da ake bincike ba.
Daga nan sai ya dora alhakin masu yi masa bi-ta-da-kulli, cewa ann dakatar da shi ne, saboda kusancin da Shugaban Hukumar, Farfesa BolajiOwansanoye ke da shi da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.
Faruk Famagham ne ya shigar da karar a madadin Obla.