Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom, ya bayyana cewa dokar haramta kiwon dabbobi da jihad kafa, ta yi tasiri sosai. Ortom ya ce an kama jimillar makiyaya 81 da shanu 3,000.
Ortom ya yi wannan karin haske lokacin da ya ke jawabin bude taron shekara ta 2019 na Kungiyar Kalilar Idoma Mazauna Amurka a Asabar da ta gabata.
“Wannan doka da muka kafa ta kawo mana zaman lafiya bakin gwargwado. Ya zuwa yau an kama makiyaya 81 kuma an kama shanu 3,000.
“Duk makiyayin da aka kama ana cin sa tara. Wadanda ke iya biya sun biya, wasu kuma har yanzu su na tsare a kurkuku.
“Ba a nan mu ka tsaya ba. Mun kara tsaurara dokar ta hanyar kama shanun da ke kiwo ko ake kiwo haka sakaka. Mu kan bayar da wa’adin kwanaki 7 mai shanu ya zo ya biya tarar kudade, sannan ya karbi shanun sa. Yanzu mu na ci gaba da karbar tarar kudaden da ake karba daga makiyayan.”
Sai dai kuma Gwamna Ortom bai fayyace mafi karanci ko mafi yawan tarar da ake cin makiyayan da aka kama shanun su din ba.
Ortom ya kara jaddada cewa a killace shanu wuri daga ba tare da yawon kiwo ba, shi ne kawai mafita daga kashe-kashen Fulani da manoma.
Ya ce karamar hukuma hudu ce kadai daga cikin kananan hukumin jihar 23 ba su afka cikin rikicin makiyaya da manoma ba a cikin shekaru shida.
Ya ce kananan Otukpo, Konshisha, Usgongo da Vandeiya ne kadai ba su dandana rikicin manoma da makiyaya ba.
Ya ce daga 2013 zuwa 2018 an yi asarar rayuka sama da 5, 000, an kone gidaje sama da 195, 000 bayan asarar bilyoyin nairori.