Yadda Gwamnatin Tarayya ta bankado ‘yan fanshon bogi 24,000

0

Hukumar Kula da Harkokin Fansho ta Kasa (PTAD) ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bankado ma’aikatan bogi har su 24,0000.

Ta ce an cire sunayen su ne daga wadanda ke karbar fansho tun bayan wani binciken kwakwaf da aka gudanar a cikin 2017.

Haka kuma ta bakin Babbar Sakatariyar Hukumar, Sharon Ikeazor, ta ce gwamnatin tarayya ta kashe naira bilyan 5 wajen biyan kudaden fanshon wata-wata ga masu karbar fansho su 300,000 daga ma’aikatun gwamnatin tarayya da hukumomin gwamnati da ta sayar da hannun jarin ta a ciki har 270.

Ikeazor ta yi wannan jawabi ne a wata ganawa da ta yi da manema labarai a lokacin da ake tantance ’yan fansho karo na hudu a Maiduguri, Jihar Barno.

Ikeazor, wadda a zaman yanzu minista ce mai jiran rantsarwa, ta ce an kashe kudaden ne wajen biyan ‘yan fansho ga wadanda suka yi ritaya daga hukumomi da ma’aikatu 270.

Ta kara da cewa hukumar ta ta bankado masu badakala da wasu iyalan mamatan da suka yi ritaya, suke ci gaba da karbar kudade, ba tare da bayyana wa hukumar su cewa sun mutu ba.

Ikeazor ta ce kafin fara tantancewar, hukumar ta karbi rahotannin mutuwar wasu ‘yan fansho tun daga 2012, wadanda kuma iyalan su na ci gaba da karbar fanshon su.

Ta kara nuna rashin jin dadin yadda ake janyo wa gwamnati asarar makudan kudade.

Daga nan sai ta yi kiran a ba wannan shiri na tantacewa goyon baya da hadin kai.

Ta ce iyalan mamata za su ci moriyar wannan tsarin tantancewa ta hanyar ko daga gida sai a biya bukata, ba tare da wata jikara ba.

Ta ce hukumar na samun hadin kai da EFCC da kuma ICPC wajen gudanar da aikin ta.

Sannan kuma ministar mai jiran rantsarwa ta ce wannan aikin tantancewa zai tantance dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 270, cikin har da jami’o’i da manyan kwalejojin ilmi da fasaha da cibiyoyin kula da lafiya da kamfanin wutar lantarki wato PHCN.

Share.

game da Author