Masana da muma masu ruwa-da-tsaki a harkokin hada-hadar cinikayya da kasuwancin amfanin gona, sun shawarci gwamnatin Najeriya ta kirkiro wani yanayi da zai samar wa manoma wata falalar inganta harkokin su a kasar nan.
Sun kawo wadannan shawarwari ne a lokacin rufe taron Masu Zuba Jari a Harkokin Noma ranar Talata a Abuja.
Hukumar Tallafa Wa Kasashe Masu Tasowa ta Amurka ce, wato USAID ta shirya taron, wanda ta tsara cewa za ta ware dala milyan 300 domin kara karfin jari ga masu harkokin noma kayan gona da ake cin moriyar su ta cinikayya da kasuwanci a jihohi bakwai.
Jihohin da za su ci ribar shirin sun hada da Kaduna, Neja, Kebbi, Delta, Ebonyi, Benuwai da Cross River.
Cikin kayan gonar da za a karfafa sun hada masara da waken soya da sauran su.
Ana ganin wannan gagarimin yunkuri zai samar da yanayi mai samar da alfanun inganta harkokin noman da ake hada-hadar cinikin sa.
Da ya ke na sa jawabin, wani masanin harkokin kasuwancin kayan gona, mai suna Yawande Sadiku, ya hawarci gwamnati ta samar da hanyoyin wayar da kan jama’a domin su san irin tallafi da tagomashin da ke tsakanin manoma da kuma masu zuba jarin hada-hadar kasuwancin su a harkar noma.
Sadiku ya ce kayan gona ne kashi 20 bisa 100 na ingancin tattalin arzikin da Najeriya ke samu a kowace shekara daya.
“Akwai bukatar a jawo hankalin masu zuba jari domin su shigo a inganta zuba jari a harkokin noma a cikin kasar nan.”
Har yau Sadiku ya ce idan za a yi aiki tare da masu sha’awar na zuba jari, to za a iya cim ma burin da ake son a gani na inganta harkokin sosai da sosai.
Shi kuma Shugaban Kamfanin Afro Food and Species, mai suna Kabir Bawa, cewa ya yi gwmnatin Najeriya ta zuba jari mai yawa a harkar noma a cikin shekaru gudu, amma har yau babu wani alfanun da za a iya tinkaho da shi, a ce an ci moriyar sa.
Daga nan sai ya shawarci masu ruwa da tsaki da su kara fadada wannan dama domin jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar su shiga su habbaka ta.
Mai magana Laoge Jayeiola kuwa cewa ya yi yawan tattaunawa tsakanin gwannati da ‘yann kasuwa masu zaman kan su zai kara taimakawa wajen fadada ci gaban wannan bangare na noma.
Daga nan sai ya kalubalanci masana su yi aikin tare da gwamnati. Domin a ta bakin sa, “Hadin guiwa da kuma tattaunawa zai kara wa yanayin damar gudanar da kasuwanci mai inganci sosai.
Ita kuwa Salamatu Suleiman cewa ta yi, bai wa leburori horo na wani dan karin ilmi zai bayar da gudummawa sosai wajen samun nasarar shirin.
“Idan aka yi kokari aka fara maida mata leburori zuwa manajojin gonaki, za su kara sanin harkokin noman sosai domin hanya ce mai gina tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a. Su na da bukatar sanin yadda ake gudanar da harkar.”
A karshe ta bayar da shawarar yin amfani da kafafen yada labarai wajen kai shirin ga mata tare da jawo hankulan matan su run rungumi shirin hannu bib-biyu.
Discussion about this post