Yadda Boko Haram suka ragargaza makarantun Islamiyya, gidaje da ofisoshin gwamnati a Gubio da Magumeri – Zulum

0

A hira da Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya yi bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ya bayyana cewa ya ziyarci fadar shugaban kasa ne domin yi masa bayanin yadda harkar tsaro ya tabarbare a jihar da kuma yadda Boko Haram suka afkawa kananan hukumomi biyu a jihar suka babbake ofisoshin gwamnati da gidajen mutane.

Zulum ya ce abin yayi muni matuka domin har makarantun islamiyya suka rika bi suna cinnawa wuta sannan kuma suka afka wa hedikwatan kananan hukumomin Gubio da Magumeri suka babbake.

” Duk da cewa rundunar soji ta nemi ta rage yawan sansanonin Sojoji a kauyuka da wurare da dama, a ganin mu duk da ba mu da kwarewa a harkar tsaro kamar su muna ganin barin shi kusa da jama’a ya fi dace wa.

” Abin da zamu maida hankali akai kuwa shine mu sama wa matasa masu zaman kashe wando aikin yi domin shine abin da yafi damun mutane sannan kuma yake ingiza matasa fadawa cikin irin wannan ayyuka na ta’addanci. Gwamnatin da ta shude ta taka rawar gani a jihar wajen da ta cancanci yabo matuka, a kan abinda suka yi za mu dora domin samun nasara wajen dawo da zaman lafiya a jihar Barno.

” Gwamnati na za ta maida hankali wajen samar musu da aikin ta hanyar kirkiro da wuraren koyon sana’o’i da kuma aikin hannu. Sannan kuma zamu taimakawa jami’an ‘yan sanda da sojoji da kuma masu farauta da ‘yan banga domin ganin an kawo karshen Boko Haram Kwata-kwata a kasarnan.

” Sannan kuma abinda ke dada ci mana tuwo a kwarya shine yadda ‘yan banga mu basu da kayan aikin da za su iya tunkarar Boko Haram. Ba zai yiwu su iya samun manyan makamai ba domin kuwa dokar kasa ta fadi wanda ke da ikon mallakan wasu ire-iren makamai. Amma kuma suma suna taikawa wajen dakile hare-haren Boko haram a lokutta da yawa.

” Wani abu da nake so in fadi kuma shine Jihar Barno na da iyaka da kasashe uku ne, kasar Chadi, Kasar Nijar da Kasar Kamaru. Duk wadannan ya sa tana da fadi a iyaka da ya zamo matsala matuka a wajen fafurar Boko Haram a Kasar nan.

” Sannan kuma duk da cewa Boko Haram ya samo asali ne a yankin Arewa Maso Gabas, a jihar Barno, yanzu abin ya wuce yadda ake zato domin ba mutanen yankin Barno ba kawai har da ma na wasu sassan jihohin nan har da na kasashen waje duk sun dulmiya Boko Haram.

Gwamna Zulum yayi kira ga mutanen da ke danganta Boko Haram da addini da su sani cewa yanzu fa ya wuce haka domin ko a harin Magumeri har da makarantun Islamiyya basu sha ba.

Share.

game da Author