Ruwan sama da aka rika shekawa kamar da bakin kwarya a ranar Abasar, ya haddasa ambaliyar da ta janyo asarar dimbin dukiya da gidaje masu yawa a Minna, Jihar Neja.
Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa na jihar Neja, Ahmed Inga ne ya kara tabbatar da haka a jiya Asabar lokacin da ya ke wa manema labarai karin haske kan ambaliyar.
Inga ya bayyana takaicin cewa kashi 75 bisa 100 na ambaliyar ta faru ne dalilin zubar da shara barkatai da jama’a ke yi.
Akwai kuma dalilin yadda haka kawai jama’a ke yawan gina gidaje da shaguna a kan hanyoyin ruwa.
Daga nan sai ya ce Hukumar sa ta sha gargadin jama’a su guji zubar da shara barkatai domin ta na toshe magudanan ruwa. Kuma su daina yin gine-gine a kan hanyar ruwa.
Ya karyata rade-radin cewa tumbatsar da ruwan dam din Bosso ne yi har ta sa ya yi ambaliya a gidajen jama’a.
Dangane da mutane uku da ake yada ji-ta-ji-tar sun halaka a cikin ambaliyar, Inga ya ce ba su da tabbacin salwantar rayukan na su, amma ana bincike domin tantancewa.
Gwamnan Riko na Jihar Neja, Ahmed Ketso, ya kai ziyara inda ya nuna jimami kuma ya ce gwamnatin jiha na da niyyar gina karin magudanan ruwa da kwalbatoci masu yawa.
Wani mai suna Abubakar Mamman, ya ce da idon sa ya ga ruwa ya ciwo wata mata ta na ta kururuwar neman agaji.
Discussion about this post