Wani binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa an kashe mutane 281 a hare-hare da kuma turnukun yakin da jami’an tsaro ke fama yi ma mahara da kuma Boko Haram a cikin watan Juli da ya gabata.
Haka kuma binciken ya kara nuna cewa a an yi garkuwa da mutane 97 a cikin watan Yuli din. Sai dai kuma binciken ya kara hasken cewa mutanen da aka kashe a cikin watan Yuli a fadin kasar nan, ba su kai yawan mutane 353 da aka kashe cikin watan Yuni ba.
Amma kuma adadin wadanda aka yi garkuwa da su a Yuli su 97, sun haura yawan mutane 60 din da aka tabbatar an yi garkuwa da su a cikin watan jiya, wato Yuni.
Idan ba a manta ba, a cikin dai watan Yuli ne Birtaniya ta gargadi duk wani dan kasar ta cewa ya kaurace wa zuwa wasu jihohi da garuruwa da ta bayyana cewa akwai barazanar tashe-tashen hankula.
Jihar Katsina ce aka fi kashe jama’a a cikin watan Yuli, inda aka yi asarar rayuka 80 a jihar, sannan an yi garkuwa da mutane 20 duk a Katsina.
Katsina ce jihar Shugaba Muhammdu Buhari, a yanzu ta zarce jihar Zamfara yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.
Katsina an kashe mutane fiye da jihar Barno a cikin watan Yuli. A Barno mutane 75 su ka rasa rayukan su, sannan aka arce da mutane shida. Benuwai an kashe mutum 30, aka yi garkuwa da mutum daya.
A FCT, yankin Abuja kuwa an kashe mutane 15 tare da yin garkuwa da mutane busu.
Jama’a da dama na ci gaba nuna damuwa da kuma nuna rashin gamsuwa da salon mulkin Shugaba Muahmmadu Buhari, musamman yadda rashin tsaro ke kara kamari.
Discussion about this post