WATA SABUWA: An cafke wasu mata da suka shahara wajen sace ya’yan mutane a Jihar Kebbi

0

Wani abin mamaki da ban tsoro da ya auku a kauyen Naima dake karamar hukumar Jega jihar Kebbi shine yadda wasu mata da suka shahara wajen sace ‘ya’yan mutane suka yi garkuwa da wata yarinya ‘Yar shekara uku.

Wadannan mata dake zama a kauyen Naima sun sace Saudatu Haruna daga gidan iyayenta tun a ranar 28 ga watan Yuli.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kebbi Garba Danjuma ya tabbatar da haka yana mai cewa rundunar ta yi nasarar ceto Saudatu daga hannun wadannan mata masu garkuwa da mutane sannan jami’ai sun cafke biyu daga cikin su.

“ Mun kama Atika Atiku mai shekaru 35 da Asiya Abdullahi mai shekaru 25 a inda suke boye da wannan yarinyar da suka sace amma kuma akwai saura da bamu kamo ba, muna nan muna farautan su.

Rundunar Puff Adder ne suka kamo wadannan mata bayan an sanar dasu bacewar wannan yarinya.

Kwamishina Danjuma yace Atika da Asiya sun tabbatar da su ne suka sace Saudatu a gidan iyayenta.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za a kai su kotu.

Share.

game da Author