‘Wasu gaggan ‘Yan Najeriya sun yi min taron-dangin ganin baya na’ – Yari

0

Mutumin da watanni uku da suka gabata shi ne shugaban kungiyar gwamnoni 36 na Najeriya, kuma wanda ya yi kaurin suna wajen yanko duk irin maganar da ya ga dama a cikin dagawa da cika-baki, a yanzu ya fara kukan subucewar mulki.

Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana cewa wasu gagga sun yi gungun ganin bayan sa.’

Kafin saukar sa mulki dai an rika yi masa kallo kuma shi ma ya rika kallon kan sa a matsayin gwamnan da ya fi sauran gwamnonin kasar nan karfi. Domin kuwa shi ne tsani tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da sauran gwamnonin kasar nan baki daya.

Lokacin ya na gwamnan jihar Zamfara, ya rika yin yadda ya ga dama, har ta kai ya zabi dan takarar gwamnan da zai maye gurbin sa a karkashin jam’iyyar APC a wani zaben ’yar-karafkiya, wanda daga karshe ya janyo wa APC asarar kowane mukami a zaben 2019 na jihar Zamfara.

Sai dai kuma soke nasarar da APC ta yi a Zamfara, wadda Kotun Koli ta yi, ta zama alheri ga al’ummar jihar, domin a cikin watanni biyu kacal har sabon gwamna Bello Matawalle ya magance fitinar ‘yan bindiga, wadda ta fitini jihar tsawon shekaru kusan goma.

‘Kukan Yari a bainar Jama’a’

Yari ya garzaya Babbar Kotun Abuja, inda ya roki kotu ta hana jami’an EFCC karafkiya a gidajen sa ko bincikar dukiyar sa.

Karnukan EFCC sun yi wa Yari kwanton-bauna ne, suka bari sai bayan ya sauka daga mulki, sannan suka yi kan sa. Suka fara yakushin sa, tare kafa masa farce, wanda hakan ya sa ya fara garza kururuwar neman ceto a Babbar Kotun Abuja.

Baya ga ci gaba da bincikar sa da ake yi, an kuma kai farmaki a gidan sa da ke Mafara, Jihar Zamfara, a kan hanyar Sokoto daga Gusau tun a ranar 5 Ga Agusta.

Yari ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja cewa EFCC sun dira gidan sa ba tare da sammacin izni daga kotu ba.

Don haka ya na so kotu ta hana karnukan EFCC shiga ko afkawa ko dirawa ko kutsawa gidan sa da kuma binciken zargin watanda, babakere, badakala da harkallar kudaden da ake yi masa.

Malami da EFCC na yi min Bi-ta-da-Kulli

Lauyan Yari mai suna Mahmud Magaji ne ya shigar da batun a kotu, a madadin tsohon gwamnan.

Yari ya na zargin Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami da EFCC ne ake amfani da su a matsayin ‘muggan makaman’ da ake yakin sa domin yi masa ganin bayan sa, bayan ya sauka daga gwamna.

Ya ce Malami da EFCC na yi masa bi-ta-da-kulli, wai kishiya na dukan kabarin kishiya bayan ta mutu an binne ta.

Duk wadannan zarge-zargen da ikirarin da Yari ya yi, haka lauyoyin sa suka shigar a Babban Kotun Tarayya a Abuja.

A cikin wannan kwafen takardar kuka da korafi da Yari yam aka a kotu, ya ce akwai gungun wasu gaggan mutanen da ke amfani da Malami da EFCC domin su ga bayan sa.

“ Wadannan gaggan manyan mutane sun yi gungun hada karfin ganin sun ga bayan wanda mu ke karewa (Yari). Saboda tuni har sun rigaya sun fassara shi a matsayin wanda ya wawuri dukiyar al’umma, ba tare da kotu ta tabbatar da hukunci a kan sa ba, a matsayin sa na tsohon gwamnan Zamfara.”

Haka dai lauyoyin Yari suka kara bayyana wa kotu a cikin takardar koken da suka maka Malami da EFCC a kotun Abuja.

Ya danganta bi-ta-da-kullin da a ke masa sakamakon rikicin da ya faru kafin da kuma bayan Kotun Koli ta soke zaben da APC ta yi nasara a jihar Zamfara.

Rikicin dai ya samo asali ne daga rigimar cikin gida da ta tirnike APC a Zamfara, tsakanin bangaren Sanata Kabiru Marafa da bangaren tsohon gwamna Yari.

‘Gungun masu Ragargaza ni’

A yanzu dai Yari ya shaida wa kotu cewa “bayan Kotun Koli ta kori APC daga zaben 2019 a jihar Zamfara, sai kuma yanzu wasu gaggan da ke jin hanushi da nukura da shi suka fito ta hanyar yin amfani da Malami da EFCC, domin su “tozarta ni kuma su dattatsa tasirin siyasa ta, su yi mata gunduwa-gunduwa.”

Abin da Yari ke so Kotu ta yi masa

Daga nan sai Yari ya roki kotu ta sa EFCC ta sakar masa mara ya samu ya yi fitsari, inda ya nemi kotun da ta:

“ Ta bada umarni ga Malami da EFCC, ta yi musu kashedin kwace masa dukiya, karbi masa dukiya, gaje masa dukiya, ko kuma kulle masa dukiya a duk inda ta ke, ko a Najeriya ko a kasashen waje, har sai an gama sauraren karar da yam aka su a kotu.

“ Kotu ta hana Malami da EFCC yi masa katsalandan ta hanyar tauye masa hakkin sa da ‘yancin sa da dokar Najeriya ta ba shi a Sashe na 34, 35, 41 da 43 wanda Kundin 1999 ta gindaya kan kowane dan kasa.

“ Kotu ta hana EFCC kwace dukkan ilahirin kudaden sa da ake cikin asusun bankunan sa a Najeriya ko kasashen waje. Da kuma kadarorin sa da ke Najeriya ko kasashen waje.”

Mai Shari’a Nkeonye Maha ya dahge sauraren karar zuwa 30 Ga Agusta.

Share.

game da Author