Mashahuriyar jaridar nan ta kasar Faransa mai suna Le Parisien, ta hakkake kamar yadda ta ruwaito cewa Barcelona na sane da cewa ba za ta iya sake sayen Neymar Junior daga kungiyar PSG ba. Amma na ta matsa lambar neman sayen sa ne kawai don ta faranta wa Messi rai kada ya fara shiga damuwar rashin gogaggun da za su taya shi taka leda a wannan kakar wasa.
Le Parisien ta yi wannan sharhi ne a yau Lahadi, inda ta nuna cewa ganin Phillippe Coutinho na kusa da kammala shirin komawa Bayern Munich, sai mahukuntan Barcelona suka maida hankali wajen kokarin dawo da Neymar zuwa Barcelona, tunda manajan sa ya nuna dan wasan na son komawa tsohon kulob din sa. Jaridar ta ce Barcelona na fama rashin nauyin aljihu a halin yanzu. Amma duk da haka ta ci gaba da matsa lambar ganin ta dawo da Neymar, wanda Leonel Messi ke jin dadin wasa da shi.
Sayen shahararren dan wasan Atletico Madrid, kuma dan wasan kasar Faransa da Barcelona ta yi, bai hana ta shan kashi a hannun Atletico Bilbao ba, a wasan farko na wannan kakar wasa ta 2019/2020.
“Zai yiwu burga da korari ne kawai Barcelona ke yi domin ta kautar da damuwa daga hankalin Messi, duk kuwa da cewa sun san bai yiwuwa su iya dawo da shi a wannan kakar La Liga ta bana.”
Kudaden da PSG ta tsawwala kan Neymar za su iya tilasta Barcelona ja baya daga batun cinikin, dama kuma ba da gaske su ke yi ba.
Musamman ganin baya ga makudan kudaden da za su biya, sai sun kara wa PSG da tukuicin wasu ‘yan wasa ba ma daya ba, iron su Ousmane Dembele, Nelson Semedo da Ivan Rakitic.
Wannan kuwa zai kasance Barcelona ta ga cewa sayen Neymar zai zame mata kamar cinikin-biri-a-sama.
Discussion about this post