Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwana al’ummar jihar Zamfara, wannan wani irin muhimmin sako ne nike son isar wa zuwa ga re ku baki daya. Wannan sako ina mai isar da shi zuwa ga reku ne tsakanina da Allah, da kuma irin yadda Allah madaukakin Sarki ya fahimtar da ni gwargwado, game da abun da yake gudana na siyasar Jihar mu mai albarka ta Zamfara. Ya ku ‘yan uwa na, zan baku wannan shawara ne, zan isar da wannan sako zuwa ga re ku ne, ba don siyasa ba, ba don maganar jam’iyyah ba, ba don wani abun duniya ba, a’a, sai dai domin kishi na ga Jiha ta, tare kuma da bakin ciki na akan matsalar tsaro da muke fama da shi, wanda alhamdulillahi, ko hasidin iza hasada yasan da cewa, da ikon Allah, yanzu gwamnan talakawa, gwamna mai ci, Dr. Matawalle yana kokari matuka akai. Muna rokon Allah har kullum, da yaci gaba da agaza masa, yaci gaba da taimakon sa, akan wannan namijin kokari da yake yi, amin.

Ya ku Zamfarawa! Ina kiran ku da cewa na farko, kuji tsoron Allah. Ku sani, ya zama dole, tilas, wajibi ku bayar da dukkanin goyon bayan ku ga wannan Dan taliki, wato gwamna Matawalle. Ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, Mahaliccin kowa da komai, Allah wanda zan tashi a gaban sa domin yayi mani hisabi. Allah wanda ina sane zan amsa tambayoyi a gaban sa, cewa ban san gwamna ba kuma bai sanni ba, ban taba ganin sa ba, kuma bai taba gani na ba, ban taba yin wata hulda da shi ba, haka shi ma bai taba hulda da ni ba. Amma ina bai tabbatar maku, wallahi wannan mutum, wato gwamna Matawalle mai kishin ku ne, mai tausayin ku ne, mai son ci gaban Jihar Zamfara ne. Sannan dukiyar al’ummah ba ita ce a gaban sa ba. Don haka wallahi, mutum irin wannan, dattijo, bawan Allah, mutumin kirki ya zama dole ku taimaka masa, ku bashi dukkanin irin nau’in goyon baya da hadin kai da yake nema daga wurin ku. Sannan wallahi, ina mai jan kunne a gare ku, ina mai gargadin ku, ina mai hada ku da Allah, da kar ku yarda da dukkanin masu yiwa wannan gwamna zagon kasa da sunan siyasa ko wani abu wai shi adawa.
Ya ku ‘yan uwa na Zamfarawa! Ku sani, dukkanin ku kuna sane da irin halin da Jihar mu ta ke ciki, na kalubalen tsaro, talauci, rashin ingantaccen ilimi da rashin abubuwan more rayuwa. Dukkanin ku kuna sane da irin halin ka-ka-ni-ka-yi, halin ni ‘ya su, halin wayyo Allah da Jihar mu ta shiga, sanadiyyar halin ko’inkula, halin cuta da zalunci, da gwamnatin da ta shude ta jefa Jihar a ciki! Mun yi addu’o’i, mun yi ta azumi da alkunuti, domin Allah ya dube mu da idon rahama, ya kawo muna canji na alkhairi, ya kawo muna shugaban da muke so, yake son mu, muke yiwa addu’a, yake yi muna; wato irin shugaban da Manzon Allah (SAW) ya siffanta a cikin Hadisin Ka’ab Dan Malik, da ke cikin Sahih Muslim. Sai ga shi Allah ya taimake mu, ya agaza muna, ya kalli kukan mu, ya ceto mu daga hannun azzalumai, ya amsa addu’o’in mu, ya kawo muna zakakuri kuma jarumin gwamna, mai son talakawan jihar sa tsakanin sa da Allah.
Daga zuwan wannan bawan Allah, wallahi duk mun ga canji, aiki ba kama hannun yaro, biyan albashi ba wasa; ya mayar da hankali sosai matuka, wurin ganin Jihar mu ta samu cikakken tsaro mai dore wa.
Sai ga shi wai an samu wasu miyagun ‘yan siyasa, wadanda sune asalin wadanda suka jefa Jihar cikin mummunan hali a can baya, saboda salon mulkin su irin na fir’auna, wai da sunan adawa, suna sukar kokarin da wannan bawan Allah yake yi. Har nike samun labari, daga majiya kwakkwara, wai wadannan miyagun ‘yan siyasa, za su yi dukkan mai yiwuwa su ga cewa wai sun kawo cikas ga duk irin kokarin da wannan bawan Allah, gwamnan al’ummah, gwamnan talakawa, Alhaji Bello Matawalle yake yi a Jihar.
Don haka, muna isar da sako zuwa ga wadannan miyagun ‘yan siyasa su sani cewa, wallahi ta Allah ba ta su ba, kuma da ikon Allah Zamfarawa ba wawayen mutane ba ne, kuma ba gidadawa ba ne, kuma ni nasan ba kidahumai ba ne. Wallahi ina sane da cewa za su yi iya kokarin su domin ganin sun baiwa wannan bawan Allah goyon baya, domin ciyar da jihar mu mai albarka gaba. Duk wani yunkuri na su na sharri, da duk wani makirci na su, da yardar Allah Subhanahu wa ta’ala ba za su taba cin nasara ba. Allah zai taimaki gwamna Matawalle da Zamfarawa da Jihar Zamfara akan su. Ai an sha mu mun warke. Irin azaba da gwale-gwale da Zamfarawa suka sha a hannun ku sun isa haka nan. Malam bahaushe yake cewa, ‘KIFI NA GANIN KA MAI JAR KOMA.’
Ya ku al’ummar Jihar Zamfara! Ku sani, lallai gwamna Matawalle na bukatar goyon bayan ku, da gudummawar ku, da hadin kan ku, domin ya kawo ci gaba mai dorewa a wannan Jiha ta mu mai albarka. Kar ku yarda da ‘yan 419 da sunan adawar siyasa, kar ku yarda da duk wani da zai mayar maku da hannun agogo baya. Ya zama dole ku so Matawalle, domin shine ya fara nuna maku kauna. Kuma shine yake son Jihar ku ta ci gaba kuma ta zauna lafiya.
Ya ku jama’ar Jihar Zamfara! Don Allah kuyi wa kan ku adalci mana, ku duba ku gani, don girman Allah yaushe rabon da ka ga ma’aikatan jihar Zamfara suna turereniya wurin sayen ragunan layyah? Wallahi har an mance da wannan a Jihar Zamfara, saboda halin tagayyara da azzalumai suka jefa al’ummah a ciki! Amma yau ka tafi Jihar, kayi fira da talakawa, kayi fira da ‘yan kasuwa, kayi fira da manoma, kayi fira da mata, kayi fira da matasa, kayi fira da ma’aikata, ka tafi kasuwa ka ga yadda ma’aikata suke murna da farin ciki. Ai wallahi yabon gwani ya zama dole!
A tarihin kirkiro Jihar Zamfara, gwamnan mulkin soja, Jibril Bala Yakubu yayi kokari matuka, a lokacin da yake gwamna. Haka, bayan shigowar siyasa, gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura shima wallahi yayi iya nasa kokari a lokacin sa. Haka nan gwamna Mamuda Aliyu Shinkafi, shima Allah ya sani, yayi kokari matuka. Amma wallahi, ina mai rantsuwa da Allah, gwamna Abdul’azizi Yari, babu abun da yayi in ba ruguzawa tare da rusa Jihar Zamfara ba! Don haka mu ba abun da zamu ce masa, illa Allah ya isa! Kuma wallahi sai Allah yayi muna sakayya akan cin amanar Jihar mu da yayi.
Mu ba ruwan mu, wallahi duk mutumin kirki zamu bayyana shi domin mutane su san shi kuma su so shi, suyi masa addu’a da fatan alkhairi. Haka nan mutumin banza zamu bayyana shi domin mutane su guje shi, kuma su yi Allah waddai da shi da mugun halin sa. Wannan shine maganar gaskiya.
Zamfarawa kuyi hattara! Gwamnan talakawa Matawalle lallai ya nuna maku halacci, saboda haka ya zama dole, ya zama tilas, ya zama wajibi ku nuna masa halacci. Kar ku yarda da duk wani mai soki-burutsu, dan 419; wanda zai nuna maku cewa gwamna Matawalle mutumin banza ne. Duk wanda ya gaya maku haka kuce karya yake yi, ko shi wanene, domin kun gani a kasa!
Allah ya taimake mu, ya zaunar da yankin mu na arewa lafiya, ya zaunar da Jihar mu ta Zamfara lafiya, da dukkanin sauran Jihohi, da ma Najeriya baki daya, amin.
Nagode,
Dan uwan ku:
Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lamba kamar haka: 08038289761 ko kuma gusaumurtada@gmail.com