UNICEF za ta dauki nauyin karatun yara mata miliyan daya a Najeriya

0

Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta tsara shiri mai suna ‘School-Based Management Committee (SBMC)’ domin saka yara mata miliyan daya a makarantun Boko da daukan nauyinsu a Najeriya.

Jami’in kula da aiyukka ta UNICEF a jihar Kano Richard Akanet ya sanar da haka ranar Talata a jihar Kano.

Akanet yace shirin SBMC zai amfani ‘ya’ya matan dake jihohin Kano, Bauchi, Zamfara, Neja, Katsina da Sokoto.

“Tun da aka fara wannan shiri UNICEF ta samu nasarori da dama ciki harda horas da manyan malaman makarantu 15,300 sannan a yanzu haka shirin na da burin saka yara mata miliyan 1.6 a makarantun boko tare da inganta makarantun arabi 42,000 domin koyar da darussan boko ga dalibai.

Akanet ya ce a binciken da suka gudanar game da matsalolin dake hana saka yara a makaratar Boko sun gano cewa kashi 44 bisa 100 na mutane suna kin saka ya’yan su a makaranta ne saboda nisan makarantun da gida.

Sannan kashi 26 bisa 100 sun koka ne cewa tsadar kudin makaranta ke hana su saka ‘ya’yan su.

Sabon Tsari

Jami’in aiyukka na UNICEF Muntaka Muktar ya bayyana cewa sabon tsarin zai suma aiki ne daga 2019 zuwa 2030 sannan a tsakanin wannan lokaci UNICEF tallafa wa makarantu da malaman arabi a jihar Kano domin koyar da darussan boko a makarantun Islamiyya dake jihar.

Mukhtar yace yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalar nisan makaranta da wasu iyayen ke kuka dashi. Sannan da rage yawan yaran dake gararamba a tituna.

“Bincike ya nuna cewa jihar Kano na da yara akalla kashi 49 bisa 100 da basu kammala makarantar boko ba.

“Sannan a jihar adadin yawan ‘ya’ya mata dake samun damar shiga makarantar sakandare (Junior) sun kai shi 47 bisa 100 sannan maza kuwa kashi 50.4 bisa 100.

“Duk da haka yara kashi 63 bisa 100 ne ke kammala karatun su na firamare inda daga ciki mata na da kashi 57.7 sannan maza 50.4.

UBEC za ta kashe Naira biliyan 2.7 don gyara makarantun firamare 2,505

Jami’in hukumar kula da ilimi (UBEC) Bello Kagara ya bayyana cewa hukumar za ta kashe Naira biliyan 2.7 domin gyaran wasu zababbun makarantun firamare 2,505 a kasar nan.

Kagara yace duk makarantar firamaren da aka zaba hukumar za ta bai wa makarantar kashi 75 bisa 100 na adadin yawan kudin gyaran da makarantar ke bukata.

A karshe Kagara ya koka bisa matsalar rashin kudi da rashin samun tallafi daga bangaren masu ruwa da tsaki a fannin ilimi wanda hakan ke kawo koma baya a fannin ilimin kasar nan.

“Rashin ware wa fannin ilimi kudi da rashin tallafa wa fannin da masu ruwa da tsakin kasar nan ke yi na daga cikin matsalolin da ke hana ‘ya’yan mu samun ilimin boko na gari sannan da hana ci gaba a fannin.”

Share.

game da Author