Wani magidanci mai suna Wasiu Badmus ya bayyanawa kotun Mapo dake Ibadan cewa ya yi da ya sanin kyale matarsa Suliyat fadawa siyasa.
`
Badmus wanda kotu ta gurfanar da shi bisa karan kokarin yin kisa da Suliyat ta shigar ya ce amincewa wa matarsa shiga harkokin siyasa ne ya haifar masa da mafi yawan matsalolin da yake fama da su a aurensa.
Ya ce ya yi kokarin nuna wa matarsa illar mace a ta shiga a na damawa da ita a siyasa amma soyayyar dake tsakaninsun ya sa ya kyale ta ta shiga siyasa sannan tun daga wannan lokaci Suliyata ta daina yi masa biyayya biyayya.
“Mun haifi yara biyar tare da Suliyat kuma ni dillalin man fetur. A wata rana ina zaune kawai sai naga wani babban dan siyasa ya zo ajiye matata a kofar gida. Tun gada wannan rana hankalina ya tashi.
“Sannan bayan haka ‘yan bangan dake unguwar mu sun sha zuwa su fada mun cewa sun ga wani babban mutum tare da Suliyat da karfe biyun na dare suna gararamba.
Badmus yace tunda a wata rana ya ji matarsa Suliyat tana shirya inda zata hadu da wani ta wayar tarho, daga nan ya rika bibiyan wanna mai yawan kiran matar sa har ya gano ashe Saurayinta ne.
“Tun bayan da na kira wannan lamba sai matata ta fusata ta ce wai ina yi mata shishhigi a harkokinta. Daga nan ne ta nemi a raba auren mu a Kotu.
Alkalin kotun Ademola Odunade Ya raba auren sannan ya amincewa Badmus da ya rike ‘ya’yan nasu a wurin sa.