Duk wani matafiyi yau da ya bi ta titin Kaduna-Abuja, daga Arewaci ko Kudancin Kasarnan ba zai taba fatan irin baƙin ciƙin da ya faɗa ba wani koda maƙiyinshi ne ya faɗa.
Tireloli ne suka rufe hanyar kwata-kwata a dalilin kashe wani direban mota ƙirar J5 wai don ya ƙi ba ɗan sanda cin hancin naira 500.
Tun bayan kashe wannan hanya kusan na awa 10 motoci na matafiya fiye da dubu ne sukayi cincirindo suka zura wa ikon Allah Ido.
Da wajen Karfe 4 na yamma ne kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar da saƙon cewa an shawo kan wannan matsala motoci sun fara wucewa.
Saidai kuma da yake motoci na ɗimɓin yawa har kusan ƙarfe 11 na dare titin a cunkushe yake kamar ba a tafiya.
Kamar yadda wakilin mu da wannan abu ya ritsa dashi ya bayyana mana, cewa” Lallai fa akwai waɗanda dole su kwana a wannan titi domin abin yayi munin gaske.”