” Baya ga suma da wasu ƙananan yara har biyu a motan da nake suka yi kowa a cikin wannan mota yayi ta kukan yunwa da ƙishin ruwa a tsawon tafiyar sama da awa 12 da muka yi a tafiyar da bai kai awa ɗaya ba.” Hafiu, matafiyi daga Enugu zuwa Sokoto.
Ita ko Elizabeth dake aikin bautar ƙasa a Abuja, tace zata tafi Kano ne domin hutun babban Sallah tare da Iyayenta sai ta faɗa cikin wannan halin ƙaƙanikayi.
” Nifa ba ya ga wannan matsala da muka faɗa ciki, wallahi tsoro na kuma masu garkuwa. Ku duba yadda mutane suke anan burjik babu iyaka, gashi kuma dama hanyar ta yi ƙaurin suna wajen yin garkuwa da mutane, kaga shikenan idan suka fito sai yadda Allah yayi.
Abu dai kamar wasa dubban matafiya ne suka maƙale cikin dandazon motoci a dalilin datse titin da hasalallun direbobin manyan motoci suka yi a titin Abuja-Kaduna.
Direbobin sun datse titin ne bayan ɗan sanda ya bindige wani direba saboda ya ƙi bada cin hancin ₦500.
Tun bayan harbe wannan direba, tireloli suka datse hanyar tun da safiyar Juma’a.
Ba a samu sun yarda sun janye motocin su ba sai wajen misalin ƙarfe biyar na yamma, wadda a wannan lokaci motoci sun fi dubu a tsaya a wannan titi sannan kuma ga wasu masu zuwa a wannan lokaci.
Haka dai hanyar ta rincabe, babu gaba babu baya.
Wakilin PREMIUM TIMES da abin ya ritsa da shi ya ce tabbas bai taba ganin irin wannan yamutsi ba.
” Mun isa farkon wannan wuri wanda bai wuce kilomita 55 zuwa Kaduna ba da misalin ƙarfe 6 na yamma, amma cikin ikon Allah bamu isa garin Kaduna sai da safiyar Allah ta’ala, ranar Asabar.
” Jama’a sun wahala matuƙa sannan, ya kai ga wasu da ke da guzirin ruwan sha suna taimaka wa wasu. Wani mai motan rake haka ya rika saidawa yana ba wasu kyata domin dai a ɗan samu a saka wa bakin salati wani abu.
Wannan datse hanya ya yi matuƙar tada wa matafiya hankali musamman ganin cewa ya auku ne a daidai ana rubibin tafiya saboda shagulgulan babban Sallah.
Wasu da dama da suka yi niyyar yin Azumin ranar Arafah sun bayyana cewa ba za su samu damar yi ba saboda basu samu damar cin komai ba tun da rana sannan ga gajiya da rashin lafiya da wasu suka kamu da.
Jama’a sun yi kira ga gwamnati da su ɗau mataki game da aukuwar irin wannan matsala a nan gaba sannan a riƙa ja wa ƴan sanda kunne matuƙa.