Garin Wurma da ke karkashin Karamar Hukumar Kurfi a cikin Jihar Katsina, ya afka cikin tashin-hankalin da ko lokacin yake-yaken sarakunan daula bai samu kan sa a ciki ba.
Tsakar daren Litinin har wayewar asubahin Talata ce wasu gaggan ‘yan bindiga suka afka Wurma, garin da ake wa kirari da “Wurma ta Dandadi, kunu sai yada”, suka yade matan aure da matasan ‘yan mata 49.
Bayan matan da suka sata, suka yi garkuwa da su, maharan wadanda sun kai kusan 300, sun mamaye Wurma a kan babura, kowane dauke da zabgegiyar bindiga.
Wurma da ke yamma da Birchi, kimanin kilomita 8 daga kan titin Katsina zuwa Dutsinma, ya hadu da ibtila’in mahara, wadanda suka rika bi gida-gida su na sungumar mata da dukiyoyi.
Majiya da dama ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun shafe sa’o’i takwas su na aika-aika, kafin su fice daga garin dauke da abin da suka kira ganima, can kusan jijjifin asubahi.
Sun rika shiga gida-gida, kamar yadda wata kwakkwarar majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa babu gidan da ba su shiga ba.
Yadda aka daka wa mata Warwaso a Wurma
Wani mazaunin garin da ya ce a boye sunan sa, ya tabbatar da cewa wajen karfe 11:30 na dare aka kewaye garin Wurma, a ranar Litinin da dare.
“ Da farko sai da suka fara yada zangon yin gangami a wani wuri, kusa da garin Tsaskiya, kuma wurin ba shi da nisa da Wurma. Kowa ya san haka.” Inji majiyar mu.
A baya, mahara sun taba shiga Wurma, suka kai hari gidan wani attajiri, har suka kwashi ‘ya’yan sa biyu, suka yi garkuwa da su.
Bayan an yi ja-in-ja din farashin diyyar da suka yanka za a biya su, sai mahaifin yaran ya shiga cikin cikin dajin da ya yi iyaka da Jihar Zamfara, ya kai naira milyan biyu, ya karbo fansar ‘ya’yan sa.
Yadda Labari ya fara Zuwa a Kunnen Mutanen Wurman
Makonni shida bayan wannan attajiri ya karbo ‘ya’yan sa, sai aka tsegunta wa mutanen garin cewa mahara na can na gangamin afkawa, kuma sun doshi garin.
Mazauna kauyen Wurma sun ce sun yi ta kiran a gaggauta kai masu ceto da dauki daga hukuma da jami’an tsaro, amma har suka yi wa garin karkaf, ko jami’in tsaro mai daure da igiyar tsumma ba su gani ba.
Baya ga bindigogi, kuma su na dauke da jikkuna cike da manya da kananan harsasai
“Sunn rika amfani da gatari da gindin bindiga sun a karya kofar duk wani gida da ke kulle.
Sun sace mana komai
Mazaunin garin ya ce sun sace duk wani abu da za su iya dauka su tafi da shi kan su tsaye, har da shanu da awaki da tumaki.
Sun kuma kwashe duk kayan abinci da na masarufin da ke cikin shaguna da kantinan garin.
“Wani mazauni garin Katsina, amma haifaffen garin Wurma, mai suna Dikko Mohammed, ya ce, “na je garin har yini na yi a ranar Laraba, amma ko tsinken ashana ba za a samu a garin ba, a yanzu haka.”
Ya kara da cewa sun yi awon gaba da dukkan baburan da suka samu a garin, kuma sun lalata duk wata mota da suka gani a garin.
Akasarin wadanda aka arce da su, duk mata ne da kuma kalilan daga kananan yara.
Dikko ya ce an sace mutane 20 daga cikin ‘yan uwan sa na jini. Kuma duk wadda aka samu da karamin yaro, to sai a hada a tafi da su duka.
Sai dai kuma da a lokacin da ya ke hira da manema labarai, Dagacin Wurma, Mustapha Mohammed, ya mutane 49 aka sace, amma daga baya an sako 12 washegari da safe.
Majiya ta kara cewa yawancin wadanda aka sace din duk iyalan wadanda ake ritsawa a gida ne, aka nemi kudi a wurin su aka rasa.
Neman Diyya
Majiya ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun karkasa wadanda suka yi garkuwar da su, kuma su na ci gaba da tuntubar dangin su batun biyan diyyar karbar su, ta wayar selula din Dagacin Wurma da suka kwace.
Wurma ta na karkashin Karamar Hukumar Kurfi, wadda aka kirkira tare da Safana, Danmusa Batsari daga Karamar Hukumar Dutsinma.
Ko bayan Karamar Sallah sai da mahara suka yi yunkurin fasa gidan mahaifin Danmajalisar Jiha mai wakiltar Kurfi, a kauyen Sabongarin-Rawayau, amma ba su yi nasara ba.
Idan ba a manta ba, shekarun baya kadan mahara sun shiga Birchi, a kan kwanar nufa Wurma, suka yi wa Dagacin Birchi kisan-gilla.
Marigayi Abdulkadir Birchi shi ne mahaifin ma’aikacin Sashen Hausa na BBC, Aminu Abdulkadir. Har yau kuma ba a san wadanda suka yi wannan aika-aika ba.