TARIN FUKA: Kira ga ƙasashen duniya da su maida hankali wajen dakile yaɗuwar cutar

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), kungiya mai zaman kanta na ‘Stop TB partnership’ da ƙungiyar dake yaki da kawar da cutar tarin fuka, kanjamau da zazzabin cizon sauro sun yi kira ga kasashen duniyan da suka fi fama da cutar tarin fuka da su maida hankali matuƙa wajen ganin sun kawar da cutar a kasashen su.

A taron kawar da tarin fuka da aka gudanar a bara kasashen duniya musamman kasashen da cutar ya fi addaba sun yi alkawarin daukan matakan kawar da cutar daga 2018 zuwa 2022.

Kasashen da suka halarci wannan taro sun bayyana cewa duk shekara za su tara dala biliyan 13 domin kawar da tarin fuka sannan kuma da dala biliyan biyu duk shekara domin inganta bincike don gano mafi ƙƴawon magungunan.

A yanzu haka tarin fuka ya fi kashe mutane a duniya fiye da zazzabin cizon sauro da Ƙanjamau.

Binciken ya nuna cewa mutane miliyan 1.6 ne suka rasa rayukan su a sanadiyyar kamuwa da wannan cuta a duniya a 2017 sannan daga cikinsu akwai mutane 300,000 dake dauke da ƙanjamau.

Tarin fuka a Najeriya

Najeriya na daga cikin kasashe 14 a duniya da wannan cuta yayi wa katutu domin binciken ya nuna cewa Najeriya ne kasa ta shida a duniya da ke fama da cutar sannan kasar ta fi yawan mutanen dake dauke da cutar a Afrika.

Bincike ya kuma nuna cewa mutane aƙalla 407,0000 ne ke kamuwa da wannan cuta a Najeriya duk shekara.

Domin dakile yaduwar cutar taron ya shawarci Najeriya kan samar da kula na gari wa mutane 1,179,600 dake dauke da cutar.

Wani Jami’I a Hukumar WHO Ayodele Awe ya ce hakan na da nasaba ne da rashin gwaji domin gano cutar da wuri,rashin ware isassun kudade domin kawar da cutar,rashin samun shugabanni masu kishin kasa,rashin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin samun damar dakile cutar da sauran su.

Awe yace bincike ya nuna cewa kashi 25 daga cikin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar a Najeriya ne ke samun magani.

Mafita

Kungiya mai zaman kanta ‘Stop TB Partnership’ da WHO sun yi kira ga shugabanin kasashen duniyan da cutar yayi wa katutu da su maida hankali wajen samarwa masu fama da cutar tallafi da kula mai nagarta.

Share.

game da Author