Yaya matsayin kasuwancin da akeyi na P.O.S a shaguna suna karɓar kwamisho a musulunci, Tare da Imam Bello Mai-Iyali
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Ina rokon Allah ya yi maka albarka a cikin rayuwarka da iyalanka, Amin.
Hakika wannan kasuwanci ya hallata domin bai sabawa tsarin musulunci ba, kuma babu riba a ciki, a fahimta ta, ai kamar aiki ka keyi sai abiyaka ladan aikinka.
Su kuma banki suna biyanka ladan janyo musu kwastoma, shi kuma mai hulda da kai yana biyanka ladan aikin da kayi masa na tura kudi ko karban kudi cikin sauki, ba tare da yaje banki ba, ko yabi layin banki, ko ya hau abin hawa zuwa ATM da sauran su.
Wannan kasuwanci mai kyau ne, kuma sauki ne ga al’umma, kuma babu riba a cikinsa, don haka halal ne.
Amma kamar yadda ko wane nau’in kasuwanci yake da halal da haram, to haramci na iya shiga cikin wannan
kasuwanci, ta hanyar Riba ko cutar da abokanin kasuwancin. Don haka
wajibi ne a kiyaye zalunci, Riba, kamayamaya da dukk hanyoyin yaudara
ko kudin ruwa.
Ayi kasuwanci mai kyau bisa yarjejeniyar cewa za’a yi maka kaza amma zaka biya kaza. Kwastoma ya sani kuma ya amince.
To idan akayi haka an tsare dokokin Allah da hakkin mutane, sana’a zatayi albarka kuma anci halal, sannan kuma ka taimaki al’uma ta hanyar saukake hadadar kuki.
Allah shi ne mafi sani. Ya Allah ka tsare mana Imanin mu da mutuncin mu. Amin.