TAFIYAR EL-ZAKZAKY: Yadda Buhari ya yi fatali da tsauraran ka’idojin El-Rufai

0

Kwararan alamomi sun nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya gwasale Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai, ya bada umarnin a bar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tafiya neman magani tare da matar sa Zeenat, ba tare da cika ka’idojin da gwamnatin Kaduna ta bijiro da su daga bayan bada belin su ba.

Da yammacin yau ne El-Zakzaky da matar sa tare da wasu tsirarun jami’an tsaro suka lula kasar Indiya a jirgin Emirate.

PRNigeria ta ji daga wata majiyar jami’an tsaro cewa ba mamaki Shugaba Buhari ya daga wa El-Zakzaky kafa tare da bada umarnin ya fita neman maganin tunda kotu ta rigaya ta bada belin sa, ba tare da cika tsatstsauran ka’idojin da gwamnatin Kaduna ta kakaba masa ba.

Zai iya kasancewa jami’an leken asirin gwamnati ne suka bada wannan shawara ta yin fatali da ka’idojin El-Rufai.

Hukumar Jami’an Leken Asiri (NIA) da kuma ta ‘Yan Sandan Ciki na DSS sun rika cuku-cukun ganin an warware wannan kwatagwangwamar tafiyar El-Zakzaky ta bayan fage, ganin cewa sun shawarci Fadar Shugaban Kasa dangane da muhimmancin cancantar amincewa da bin umarnin kotu.

Hakan ya kara biyo baya ne ganin kuma cewa an yi amfani da tattaunawar diflomasiyya da wasu kasashe, ciki har da gwamnatin Iran a kan lamarin.

GWAMNATI TARAYYA TA GWASALE SHARUDDAN ‘SHIRMEN’ GWAMNATIN EL-RUFAI –Femi Falana

Da ya ke zantawa da PRNigeria, lauyan El-Zakzaky, Femi Falana, ya shaida wa jaridar cewa gwamnatin tarayya ta yi wancakali da sharuddan ‘shirmen’ da Gwamnatin Jihar Kaduna ta nemi kakaba wa shugaban mabiya Shi’a din da kuma matar sa Zeenat kafin a bari su tafi Indiya a yau Litinin.

Falana ya ce sharuddan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kakaba wa El-Zakzaky kwata-kwata ba ‘ya’yan cikin dokar kasa ba ne, ‘ya’yan agola ne Kaduna ta nemi maidawa ‘ya’yan dokar kasa na halas.

Sanannen lauyan ya ce tunda kuwa sharuddan sun duk harankazama ce, ba su cikin ka’idojin bada beli da tafiya kotu wadanda kotun Kaduna ta gindaya, babu yadda za a yi kotu ta amsa bukatar gwamnatin Kaduna, har ta amince da tsauraran sharuddan.

Falana ya kara hasken cewa babu yadda za a yi ma gwamnati ta tsaya bin wasu sharudda da gwamnatin Kaduna ta kakaba, domin DSS sun rigaya sun fito sun bayyana wa duniya cewa za su bi umarnin kotu, su saki El-Zakzaky da matar sa su fita zuwa Indiya neman magani.

Gwmnatin Kaduna dai ta bada sanarwar amincewa da belin El-Zakzaky da kotu ta yi, amma kuma ai ta bijiro da wasu tsauraran ka’idoji, wadanda masana shari’a ke ganin shiga hurumin kotu ne, kuma ba su cikin ka’idoji.

TSAURARAN KA’IDOJIN KADUNA DA GWAMNATIN TARAYYA TA YI FATALI DA SU

Gwamnatin Kaduna ta nemi kotun ta kakaba wa malamin wasu sharudda kafin ta bar shi ya fice zuwa Indiya. Sharuddan sun hada da:

Sai Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ga hujja daga Asibitin Medanta na Indiya, cewa lallai can din ne za a duba lafiyar su El-Zakzaky, kuma sai an tsara sharuddan amincewar su cewa da sharuddan tafiya neman magani a bisa tasarin diflomasiyya.

Masu tafiya neman maganin a tabbatar sun sa hannun amincewa cewa idan sun warke za su dawo Najeriya su ci gaba da fuskantar shari’ar da suke yi. Sannan kuma su da kan su ne za su dauki nauyin kudin tafiyar su da na dawowar su, kudin yi musu magani da kudin hidindimun zaman su a Indiya a tsawon lokacin da za su yi a can.

Dole su kawo masu belin da za su tsaya musu, mutum biyu wadanda za su iya gabatar da su a duk lokacin da aka neme su. Daya daga cikin masu belin ya kasance basarake ne mai daraja ta daya dan jihar Kaduna. Daya kuma ya kasance sananne ne a jihar Kaduna. Dukkan su biyu din su kasance su na da gida a cikin Jihar Kaduna.

Gwamnatin Najeriya ta samu tabbataci a rubuce daga Gwamnatin Indiya cewa idan su El-zakzaky sun nemi a ba su mafaka, to ba za ta bas u ba. Sannan kuma ta haramta musu gudanar da duk wasu aikace-aikacen da abin da ya kais u kasar ne su yi ba. Musamman abin da zai zama barazana ga Najeriya.

Su rubuta takardar amincewa ta hannun lauyoyin su cewa idan sun je Indiya ba za su yi wasu abubuwan da za su zama barazana ko cutarwa ga ci gaba da shari’ar su da ake yi ba, ko barazana ga tsaron kasar nan da kasar Indiya.

Jami’an tsaro daga Najeriya su raka su zuwa Indiya neman magani, kuma su kasance tare da su a iya tsawon lokacin da za su kasance a Indiya, har dawowar su Najeriya.

Sai Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Indiya ya amince kuma ya tantance duk wani wanda zai kai musu ziyara a asibiti tukunna kafin a bari ya gana da su.

Yanzu dai hukuma ta amince zai tafi kenan.

Share.

game da Author