Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-naden shugabannin wasu ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Wadanda aka nada sune:
1 – Basheer Garba Mohammed – Kwamishina a Hukumar Kula ‘yan gudun hijira, masu neman mafaka da bakin haure.
Bashir ya canji Sadiya Umar Farouk, da aka yi mata minista daga jihar Zamfara.
2 – Chioma Ejikeme – Bababn Sakataren Hukumar ayyukan ma’aikatun Fansho – Ta canji Sharon Ikeazo
3 – Kashifu Inuwa Abdullahi – Darekta janar na Hukumar NITDA – Ya canji Isa Pantami da aka yi wa Minista.
Bayan haka Buhari ya aika da sunan Adeleke Moronfolu Adewolu majalisar dattawa domin zama kwamishina a Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC).