Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin mataimaka guda uku.
1 – Hajo Sani – Babban maitaimaka wa ta musammman kan Ayyukan gwamnati
2 – Hadi Uba – Mai taimakawa na musamman kan Ayyukan gwamnati
3 – Kamal Abdurrahman Muhammmed – Mai taimakawa na musamman kan kiwon Lafiya
Duka wadannan nade-nade zasu yi aiki ne a ofishin Uwargidan Shugaban Kasa.
Haka kuma Ita Enang dake aiki a ofishin shugaban Kasa wanda shine mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin Majalisa bangaren Majalisar dattawa ya zama Mai ba shugaban Kasa Shawara kan harkokin yankin Neja-Delta.
Discussion about this post