Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Femi Adesina babban mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, sannan kuma da Garba Shehu a matsayin babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai.
Bayan haka Buhari ya amince da nadin Laolu Akande a matsayin mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai.
Sauran sun hada da:
1 – Tolu Ogunlesi -Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na zamani
2 – Bashir Ahmad – Mataimaki na musamman kan sabbbin kafafen yada labarai
3 – Lauretta Onochie – Mataimaki na musamman kan Kafafen sada zumunta ta Soshiyal Midiya sannan da Nazir Bashiru.
4 – Buhari Sallau – Mataimaki na musamman kan kafafen yada labari na Talabijin da Radiyo