Sojoji sun kashe ‘yan sanda uku, sun saki gogarman masu Garkuwa da mutane a Jalingo

0

A wani abin tashin hankali da ban tsoro da ya auku a hanyar Ibi zuwa Jalingo, dake jihar Taraba ranar Laraba shine yadda gungun sojoji suka yi wa tawagar ‘yan sandan kwantar bauna suka kashe ‘yan sanda uku.

Frank Mba ya bayyana haka a takarda da ya fitar ranar Laraba cewa sojojin sun budewa ‘yan sandan wuta ne bayan sun kamo wani gogarman masu garkuwa da aka dade ana farautar sa mai suna Alhaji Hamisu.

Frank yace Hamisu yayi kaurin suna a wannan yanki wajen yin garkuwa da mutane.

‘Yan sandan sun farwa maboyar sa ne inda suka kamo shi zasu kai shi garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

” Jami’an ‘yan sandan sun isa shingen sojojin ne inda da ganin su sai suka bude musu wuta duk da sun gane cewa ‘Yan sanda ne ke tahowa. Bayan sun kashe uku daga ciki sai suka saki Alhaji Hamisu a wannan daji.

Sufeto janar din ‘Yan sanda Mohammed Adamu ya bayyana cewa tuni har an aika da babban mataimakin shugaban ‘Yan sanda DIG zuwa Jalingo domin yin bincike kan abinda ya faru. Su kuma wadanda aka kashe tuni an aika da gawarwakinsu dakin ajiye gawa.

Share.

game da Author