Sojojin Najeriya sun kama wasu shirga-shirgan motocin yaki da ba a san ko daga ina suka shigo kasar nan ba a Jihar Adamawa.
Sojojin dake Birged na 23 suka kama wannan jerin manyan motocin a karamar hukumar Fufure.
Sai dai kuma ba ba san ko daga ina wadannan motoci suka tsallako Najeriya ba domin ba ma irin motocin sojojin Najeriya bane.
Tuni dai ma’aikatan tsaron kasa ta aika da jami’ai da ayi bincike akai sannan an mika motocin ga hukumar kwastan na kasa reshen jihar Adamawa.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya wannan jarida PREMIUM TIMES HAUSA ya buga labarin yadda aka tsohon gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ya shigo da manyan bindigogi masu tarin yawa da harsasai.
Wannan badakala ya kai ga har an fara zargin gwamnan da shirya wani abin da ba haka ba.
Har yanzu dai ba a ce komai akai ba kuma gwamnati bata tuhumi wannan tsohon gwamna ba.