SHAWARA: Za a yiwa ‘yan Jihar Ebonyi Allurar Rigakafi

0

Gwamnatin jihar Ebonyi za ta yi wa yara da manya a jihar Rigakafin Zazzabin Shawara a duk kusurwar jihar.

Gwamnati ta ce za ta yi wa yara ‘yan watanni tara har zuwa manya masu shekaru 44 allurar rigakafin cutar a kananan hukumomi 13 dake jihar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Daniel Umezurike ya sanar da haka wa manema labarai ranan Litini.

Umezurike ya ce gwamnati ta kuma hada hannu da kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen kasarnan domin samun nasarar haka.

“Domin dakile yaduwar cutar gwamnati ta hada hannu da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC), Ma’aikatar kiwon lafiya da Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta kasa (NAPHCDA) domin yi wa mutane allurar rigakafin cutar.

Idan ba a manta ba a bara ne Jami’ar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar WHO za ta ba Najeriya gudunmawar maganin allurar rigakafi zazzabin shawara har na miliyan 12 a shekarar 2018 sannan ta kara bada magani na miliyan 19 a 2019.

Charity ta bayyana haka ne a Abuja inda ta kara da cewa WHO za ta samar da wannan gudunmawa ne da hadin guiwar Kamfanin GAVI.

Charity ta ce suna kokarin ganin an kau da wannan zazzabi zuwa 2026.

Share.

game da Author