SHARI’AR EL-ZAKZAKY: An tsaurara matakan tsaro a Kaduna

0

Rundunar ‘ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samar da tsaro a garin Kaduna da kewaye a yayin ci gaba da shari’ar El-Zakzaky da za a yi ranar Litinin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya ce an samar da tsaro a ko ina a faɗin jihar yana mai cewa jama’a su fito domin gudanar da al’amurorin su.

Sai dai kuma ya bayyana cewa an saka tsauraran matakan tsaro a wasu manyan tituna dake kusa da babban kotun Kaduna.

Sabo ya tunatar da mutane game da haramcin gudanar da zanga-zanga ko tattaki a jihar yana mai cewa doka hana haka nan a jihar.

” Jami’an tsaro ba za suyi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda ya nemi ya karya wannan doka a jihar.

A ranar litinin ne kotu a Kaduna za ta yanke hukuncin neman a ba shugaban kungiyar Shi’a Ibrahim El-Zakzaky dake tsre tare da Matar sa beli domin ya garzaya asibiti a duba lafiyar sa.

Share.

game da Author