Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin fara aikin yi wa yara rigakafin shan inna a fadin jihar.
Jami’a a ma’aikatar Kiwon lafiyar na jihar, Abimbola Folorusho ta sanar da haka a Ilorin ranar Alhamis.
Kananan hukumomin da za a fara da su sun hada da Asa, Baruten, Ifelodun, Ilorin ta kudu, Ilorin ta yamma, Ilorin ta gabas da Moro.
Za a fara rigakafin ne a wadannan kananan hukumomi daga ranar 3 zuwa 23 ga watan Agusta.
Folorunsho ta ce lallai yin rigakafin zai taimaka waje samar wa yara kariya daga kamuwa da cutar wanda shine babban dalilin amida hankali akai da gwamnatin jihar tayi.
Bayannan ta yi kira ga iyaye da su maida hankali sannan su mika yayan su idan aka zo yi musu wannan rigakafi.
Idan ba a manta ba kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya yi kira ga kasashen duniya da su maida hankali wajen kiyaye yin allurar rigakafi a kasashen su.
Kungiyar ta yi wannan kira ne bayan binciken da ta yi tare da hadin guiwar asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) a 2018.
Sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu akwai akalla yara miliyan 20 da ko ba suyi alluran ba ko kuma ba su yi duka alluran ba.