Kotu a jihar Barno ta yanke wa shugaban makarantar sakandaren Dala dake garinMaiduguri Josephine Udeh hukuncin daurin shekara daya a kurkuku idan hara ba zata iya biyan kudin belin da aka yanka mata ba.
Alkali Aisha Kumaliya ta bada belin Josephin akan naira 150,000 ranar Alhamis.
An kama shugaban makarantar ne da laifin waushe kudin jarabawar dalibai na WAEC har naira miliyan biyar.
Sai dai kuma ko da kotu ta fara zama domin sauararen karar wanda hukumar EFCC ta shigar a watan Afrilu Josephine ta musanta aikata haka duk da dimbin hujjojin da aka bayyana karara a Kotu.
Sai kuma daga baya sai ta amsa laifi sanna tace a shirye take ta biya wadannan kudade.
Daga nan dai lauyan dake kare Josephine, B.G Sanda ya roki sassauci a wajen kotu ganin cewa Josephine ta amsa laifinta sannan ta amince ta biya kudin da ta waske da su.
Alkali Kumaliya ta bada belin Josephine kan Naira 150,000.
Discussion about this post