Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku jama’ah, lallai mu sani, hassada mugun ciwo ce da idan Allah ya jarabi bawa da ita to ya gama yawo, kuma sai dai wani ba shi ba. Zai lalace, zai balbalce, zai rasa abin yi a rayuwar sa in ba damuwa da dawwama cikin bakin ciki ba! Domin zai karar da rayuwar sa wurin bibiyar rayuwar wadanda yake yiwa hassada. Sannan duk alkhairin su ba zai taba ganin sa ba, abin da kawai zai nema na su har kullun, shine, ina suka yi kuskure, ina suka kasa, ina suka gaza, ina ne suka yi ba daidai ba; wannan kawai shine abin neman sa, amma alkhairan su, sam babu ruwan sa da wannan, idan ma ana fadar alkhairin su, sai yaji kamar ya mutu, sai yaji kamar ya kama da wuta. Wannan shine dabi’ar duk wani Hasidin iza hasada.
Ya ku jama’ah, wallahi tunda adalin Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya zama Sarki, Matukar yana gari bai yi tafiya ba, ba ya rabuwa da karbar baki iri-iri, daga ko wane sashe na duniya. Wannan ba yin sa bane, al’amarin mun san daga Allah ne, baiwa ce daga mai duka, wato mahaliccin kowa da komai!
To sai kwatsam, a wannan karon mu ka ga salo ya canza. Domin mun fahimci cewa yanzu ya samu mai yin gasa da shi cikin daukaka da baiwar da Allah yayi masa ta jama’ah.
Domin kowa ya sani, cikin kwanakin nan, Ambassador na Kasar Faransa a Najeriya, ya kawo wa Mai Martaba Sarki ziyarar girmamawa har gida, suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Abin mamaki, kawai sai na hangi Malam babba na kofar gabas, shima wai ya bazama, ya kaiwa wannan Ambassador ziyara har Embassy din sa. Hmmm! Ikon Allah sai kallo!!
Sannan ba’a dade ba kuma General Yusuf Buratai, Shugaban Hafsan sojojin Najeriya, shima ya kawo ziyarar ban girma har fada, ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
Haba wa, kan kace me, Malam babba na kofar gabas, tuni ya shuri takalmin sa, shima yakai wannan ziyara har gida, Abuja, ga General Buratai.
To, anan, abinda nike so Malam babba na kofar gabas ya sani, shine, sunayen Allah Guda biyu suna yin tasiri a kan kowane mai mulki da ko wane Shugaba.
Idan jagora ya zama mai adalci, to za ka ga tasirin المعز (Almu’izzu) na aiki akan sa, sai kowa ya zama yana kaunar sa kuma yana neman sa cikin al’amurran sa, dama kuma Allah yace: وتعز من تشاء.
Idan kuwa Shugaba ya zama azzalumi, to inda duk zai shiga wannan suna na المذل (Almuzillu) shine zai ta yin tasiri akan sa, zai yi bakin jini, sannan ba za’a neme shi a wurare masu daraja ba. Ko ya nemi yin mu’amala da masu daraja, ba za’a zauna da shi cikin darajar ba, kasancewar siffar kaskanci, saboda baya yi wa jama’ar sa adalci, tana bibiyar sa a ko’ina yake. Allah yace: وتذل من تشاء.
Don haka, ina kira ga dukkanin Al’ummah, da kada mu yarda mu zama masu hassada ga dukkan wanda Allah yace lokacin sa ne. Domin ko meye za kayi akan ka dakushe wannan daukakar ta sa, wallahi ba za ka taba yin nasara ba, domin al’amarin ba yin sa ba ne, yin Allah ne. Sannan kuma a karshe, kai ne dai za ka fadi kasa warwas! Muna sane da tarihin Annabi Musa da Fir’auna da ‘ya ‘yan Annabi Adamu da ‘ya ‘yan Annabi Ya’kub su Annabi Yusuf da ‘yan uwan sa da tarihin Annabi Muhammad (SAW) da dukkan masu yi masa hassada; kai da tarihin dukkanin masu hassada, tun farkon duniya har zuwa yau kuwa. Mun ga cewa basu yi nasara ba. Don haka, sai mu kiyaye, kuma muyi hankali.
Kada kace za ka bibiyi manya wai domin kayi suna, a’a, kai dai ka yarda cewa ita daukaka daga Allah ta ke zuwa. Idan Allah yace kai wani ne, to wallahi kowa sai yazo har inda kake ya gaishe ka, ba tare da kai ne ka nemi hakan daga gare su ba!
Ya ku ‘yan uwa na masu kima, masu girma, masu daraja, masu albarka, ku sani, mun sha fada maku kuma mun sha nanatawa maku cewa, ba Mai Martaba Sarkin Kano kawai ba, wallahi dukkanin Sarakunan mu na arewa, Musulmi, jagorori ne ga Addinin mu mai albarka na Musulunci. Shehu Usmanu Dan Fodio Allah ya jikan sa da rahama, shine sanadiyyar samar da su, kuma shine ya kafa su, kafin turawa shedanu da shedanun wasu daga cikin ‘yan bokon mu da shedanun wasu daga cikin ‘yan siyasar mu su hada kai da nufin tozarta su. Don haka, mu wallahi a kan abun da Allah Subhanahu wa ta’ala ya fahimtar da mu, taba su taba Addini ne, cin mutuncin su cin mutuncin Addini ne, tozarta su tozarta Addini ne. Kamar yadda a daya gefen kuma girmama su, da mutunta su muke kallon sa a matsayin mutuntawa da girmama Addinin Allah. Don haka duk wanda yake ganin ba haka bane, to ya rage nashi, ya je can yayi tayi da wannan gurguwar fahimta ta shi! Kuma mu dai ya sani, sam bamu tare da shi har abada, a cikin wannan jahilar fahimta ta shi da yardar Allah.
Abun ayi kuka, abun kunya, abun bakin ciki, kuma abun mamaki; ‘yan siyasar kudu kullun suna ta kokarin yaya za’a yi su ciyar da al’ummar su da yankin su gaba, mu kuwa namu wasu ‘yan siyasar har kullun sai kokarin fada da Sarakunan mu masu daraja, tare da kokarin keta rigar mutuncin da magabatan mu suka bar muna, da muke alfahari da su. Kaico! Allah wadaran naka ya lalace, wai rakumin dawa yaga na gida!!
Ina rokon Allah ya taimaki Sarki da dukkanin Sarakunan mu da masarautun mu, Ya Allah ka karawa Sarki lafiya, Imani da nisan kwana, amin.
Allah yasa mu gane, kuma yasa mu dace, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.
Discussion about this post