SALLAH: Maɗigo da Luwadi ne suka Jefa Najeriya cikin matsalar rashin tsaro – Inji Sarkin Gwandu

0

Sarkin Gwandu kuma shugaban sarakunan kasar Kebbi, Mohammadu Bashar ya bayyana cewa yawaita aikata ayyukan ashsha da mutane ke yi yanzu ne ya jefa Najeriya cikin halin da muke ciki na rashin tsaro.

Sarkin Gwandu ya fadi hakane da yake jawabi a filin Idi bayan kammala Salƙar Idi.

” Aikata ayyukan alfasha da suka haɗa da madigo da mata ke yi yanzu da luwaɗi sune suka sa muke ta fama da matsaloli dabam-dabam a ƙasarnan.

Sarki Bashar ya ƙara da cewa idan ba dawowa ga Allah jama’a suka yi ba, za a ci gaba da faɗawa cikin matsaloli na tashin hankali, kashe-kashe da rashun zaman lafiya a ƙasarnan.

Sannan kuma ya yi kira ga mutane da su ci gaba da yi wa ƙasarnan addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba.

A jawabin sa, Gwamnan jihar Kebbi ya jinjina wa shugaba Muhammadu Buhari kan saka hannu a kudirin maida kwalejin koyon ayyukan gona zuwa Jami’a.

An yi sallah lafiya a Kebbi.

Share.

game da Author