Fitaccen dan wasan Liverpool Mohammed Salah ya zura kwallaye biyu a ragar Arsenal a yagalgalasu da tayi a wasan ranar Asabar.
Arsenal sun jefa kwallo daya a ragar Liverpool sai dai kash abun da kamar wuya domin baya ga kwallaye biyu da Salah ya jefa Joel Matip ya jefa kwallo daya.
Wasa dai ya tashi 3-1.
Itama kungiyar Manchester bata sha da dadi ba domin Crystal Palace ta biyo su ne har gida ta basu kashi.
An tashi wasa 1-2 a Manchester.
A cikin wasanni 6 da aka buga a ranar Asabar, Liverpool ce kawai ta yi nasara a gida duk sauran sun sha kashi ne a gida in da baki suka yi nasara.