SAKACI: Yadda Gwamnatin ‘Yar’Adua, Jonathan da Buhari ke neman janyo wa Najeriya asarar naira Tiriliyan 3.2

0

Ranar Juma’a da ta gabata ne Kotun Sauraren Kararrakin Kasuwanci da Cinikayya ta Birtaniya, a karkashin Mai Shari’a J. Butcher, ta yanke hukuncin yanka wa Najeriya diyyar tarar dala bilyan 9.

Butcher ya umarci Najeriya ta biya kamfanin P&ID, wato Process Industrial Development Limited, zunzurutun kudade kwatankwacin naira tiriliyan 3.7.

Wadannan kudade an yanka wa Najeriya biyan su a matsayin karya yarjejeniyar kwangila da ta yi, tsakanin ta da P&ID.

Wannan kwangila dai tun zamanin mulkin Marigayi Umaru Yar’Adua aka bada ta. Amma daga bisani ta zama alakakai, har rikicin ya mirgina zuwa kotun Birtaniya.

DALLA-DALLA: Bayanin dangane da kokarin karya arzikin Najeriya Warwas

1 – An kakaba wa Najeriya biyan diyyar ce saboda kin cika alkawarin da ta yi, inda ta karya jarjejeniyar kwangila. Wannan laifi da aka tuhumi Najeriya da yi, ya haifar da dimbin asara ga kamfanin P&ID.

2 – Kwangila ce ta harkar gina masana’antun sarrafa gas da aka cimma yarjejeniya tun cikin gwamnatin marigayi Umaru ’Yar’Adua, cikin 2010.

3 – An ci Najeriya tarar a karkashin Dokar Haramcin Karya Yarjejeniyar Kwangiloli ta Ingila da Wales, ta 1996, da kuma Dokar Haramcin Karya Yarjejeniyar Cinikayya ta Najeriya, mai lamba: CAP A18 LFN ta shekara ta 2004.

4 – An yanke hukuncin ne bayan Najeriya ta shafe shekaru sama da biyar ta na sakacin kin daukaka kara.

5 – Idan har Najeriya ta kasa yin nasarar shawo kan wannan gagarimar matsala ta hanyar sasantawa ko kuma sa’ar yin nasara idan ta daukaka kara, to za a kwace dukiyar Najeriya da ke bankunan Ingila da Amurka, har kwatankwacin dala bilyan 9, wato naira tiriliyan 3.2 kenan, a damka wa kamfanin P&ID.

6 – Akwai matsaloli da mishkiloli a cikin kwangilar, wadda tsohon Ministan Fetur na zamani Umaru Yar’Adua, Rilwanu Lukman ya sa wa hannu. An sa wa kwangilar hannu a lokacin da Umaru ba shi da lafiya, ya na ta hakilon neman lafiyar sa tsakanin Ingila da Saudiyya.

7 – Kotu ta rattaba hukuncin ne tun cikin 2015, watanni biyu bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki.

8 – Shugaban lokacin Goodluck Jonathan ya bar wa Buhari gadon warware matsalar, saboda har ya sauka lauyoyin Najeriya sun tsaya Turanci, maimakon maida hankali wajen warware matsalar.

9 – Buhari ya yi sakacin rashin nada ministoci kan lokaci, wanda hakan ya sa Najeriya ta rasa ministan shari’a da zai bai wa Buhari shawara cikin gaggawa dangane da yadda za a shawo kan lamarin, kafin kotu ta yanke hukunci.

10 – Wadanda su ke kewaye da Buhari a lokacin, watau fadawan sa ‘yan-ba-ni-na-iya, sun nuna masa cewa matsalar gwamnatin PDP ce.

11 – Duk da cewa a yanzu Najeriya ta farka daga likomon gare da ta ke yi, ta na ta gwagwagwar ganin ta yi nasarar rashin biyan diyyar, duk wanda ya nakalci yadda rigimar ta ke, zai tabbatar da cewa da wahalar gaske dan akuya ya kayar da kura a kokawar tsakiyar dokar jeji.

12 – Najariya ta yi sakacin gaske tun daga zamanin Yar’Adua da Jonathan har zuwa yanzu zamanin Buhari. Saboda a wannan kasar ba a dauki karya doka ko karya yarjejeniya a matsayin babban laifi ba, su Turawa bah aka su ke ba.

13 – Haka ba a damu da hukunta manyan da suka karya doka a Najeriya ba, kamar yadda Najeriya ba ta damu ba idan ta karya doka a cikin kasar ta.

14 – Kasashen Turai sun dauki komai da muhimmanci. Inda wani ya yi rawar banjo a Najeriya aka ba shi kudi, idan ya yi wannan rawar a wata kasa, to dukan tsiya zai sha.

KWANGILAR GAS: Yadda Kilu Ta Jawo Wa Najeriya Bau

1 – Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanin P&ID, mallakar wadansu Turawa biyu, Micheal Quinn da kuma marigayi Brendan Cahill. Kamfanin ya kai shekaru 30 da kafuwa, kuma kwararre ne wajen iya aikin sa.

2 – An kulla yarjejeiyar tsakanin PID cikin watan Janairu, 2010 domin gina masana’antar sarrafa gas a Najeriya. Kwangila ce aka kulla ta tsawon yarjejeniyar shekaru 20.

3 – Rilwanu Lukman, wanda ya rasu cikin 2014 ne ya sawa kwangilar hannu a matsayin sa na Ministan Fetur lokacin Umaru Yar’Adua ya na kwance asibitin Saudiyya ya na jiyya.

Yaya aka kulla Yarjejeniyar Kwangilar?

1 – An kulla cewa Najeriya ke da kashi 85 bisa 100 na tataccen gas wanda za a rika amfani da shi wajen samar karfin hasken lantarki da inganta masana’antu.

2 – Shi kuma P&ID zai rika karbar kashi 15 bisa 100 kenan tare da cin moriyar sinadaran ‘methane, ‘propane’ da ‘butane’, wadanda za su rika fitarwa kasashen waje.

3 – Ita ma Najeriya za ta amfana da kashi 10 bisa 100 daga sinadaran uku da P&ID zai rika fitarwa su sayar a kasashen waje.

Ka’idojin da Najeriya da P&ID suka gindaya wa juna

A cikin wannan jarjejeniya dai akwai cewa: Najeriya za ta rika samar da gas mai yawan ma’aunin scf milyan 150 ga masa’antar wadda P&ID za ta gina. Idan tafiya ta yi nisa kuwa, za a kai har ana samar wa masana’antar da gas jejin scf milyan 400. Kamfanonin hako mai ne ke samar da gas a kasar nan.

Yadda aka fara yi wa kwangilar ‘SHILLON-BILYA’

1 – An amince a rubuce cewa Najeriya za ta gina ko ta shimfida bututun da za a rika tunkuda gas zuwa masana’antar da P&ID zai gina a Adiabo, cikin Karamar Hukumar Odukpani, a Jihar Cross Rivers. Gwamnati ce za ta rika samar wa P&ID gas din da kan ta, daga rijiyar mai ta OML 67 da ta 123 wadda kamfanin Addax Petroleum ke har mai a ciki.

2 – To daga nan ne labari ya sha bamban, al’amurra suka sakwarkwace, ko kuma aka sakwarkwatar da al’amurran.

3 – Ita dai Najeriya ba ta gina ko shimfida bututun a karkashin kasa zuwa inda P&ID ya ce a kai mata su ba.

4 – Sai P&ID ya ce ya kashe dala milyan 40 wajen aikin gina masana’antar gas, wadda kuma rashin shimfida bututun gas da Najeriya ba ta yi ba, babban laifin karya yarjejeniyar kwangila ta duniya ce.

5 – An kasa warware wannan matsala a lokacin Jonathan, domin bayan kulla yarjejeniyar Umaru bai dade a kan mulki ba, ya rasu.

6 – Cikin watan Agusta, 2012, sai P&ID ya fusata, ya maka Najeriya kara a Kotun Bin Diggidin Karya Jarjejeniyar Kwngila a Cinikayya a London.

7 – P&ID ya nemi kotu ya tilasta wa Najeriya biyan ta diyyar asarar da ta tabka, ciki kuwa har da kirdadon irin ribar da za ta samu a tsawon shekaru 20 na tsawon yarjejeniyar duk kamfanin ya nemi Najeriya ta biya shi.

Yadda Jonathan da Buhari suka gaji Alakakai

1 – A lokacin Jonathan an yi kokarin sasantawa, inda P&ID ya nemi a biya shi diyyar dala bilyan 1.5, amma a karshe ya amince da zai karbi dala milyan 850.

Wannan sasantawa ta samu tsaiko, saboda Jonathan bai yi nasarar zabe a 2015 ba. Tilas ya bar wa gwamnatin Buhari mai jiran hawa mulki a lokacin cin gadon yadda za ta warware wannan kwatagwangwama. Dama shi ma Jonathan ya tsaya jan-kafa ya na neman a rage kudin daga dala milyan 850 zuwa kasa da haka, har ya sauka ba a cimma matsaya ba.

Buhari ya yi sakacin rashin nada ministoci kan lokaci, wanda hakan ya sa Najeriya ta rasa ministan shari’a da zai bai wa Buhari shawara cikin gaggawa dangane da yadda za a shawo kan lamarin, kafin kotu ta yanke hukunci.

Da yawan masu sharhi sun tafi a kan cewa wadanda su ke kewaye da Buhari a lokacin, watau fadawan sa ‘yan-ba-ni-na-iya, sun nuna masa cewa matsalar gwamnatin PDP ce. Saboda a lokacin bai nada ministoci da wuri ba.

Katsam, cikin watan Yuli, 2015, watanni biyu bayan hawan Buhari, sai kotu ya yanka wa Najeriya biyan P&ID diyyar dala bilyan 6.6, sai kuma karin wata dala bilyan 2.3 da kotu ta amince cewa su ne kiyasi ko kirdadon ribar da P&ID zai iya samu a tsawon shekaru 20 ya na huldar da Najeriya, idan da yarjejeniyar ta tafi salum-alum, yadda aka gindaya.

BUHARI – Gaba Kura Baya Siyaki

A gaskiyar magana, Buhari bai dade da hawa mulki ba sai farashin danyen mai ya karye a kasuwannin duniya. Sannan kuma naira ta rika yin faduwar ‘yan bori da duk lokacin da ta yi arba da dalar Amurka.

Sai dai kuma da daman a ganin cewa shi ma ya yi sakaci, domin idan ya na ganin ba zai iya biyan P&ID ba dala milyan 850 ba, zai iya neman sassauci, don kada a bari ta sake garzayawa kotu a lokacin.

Ga shi kuma a lokacin ana halin walle-walle, har jihohin kasar nan ba su iya biyan albashin ma’aikatan su.

Ina Mafita?

Babu wata mafita sai dai Najeriya ta sake neman zama teburin sasantawa da P&ID, domin matsawar hukuncin da kotun Landan ta zartas ya tabbata, kuma Kotun Amurka ta rattaba irin wannan hukunci a kan Najeriya, to za a tatsi wadannan makudan kudade daga asusun gwamnatin tarayya na Ingila da Amurka ta dankara wa P&ID.

Amma kuma yanzu Gwamnan Babban BANKIN Najriya, Godwin Emefile da Babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a, sun sha alwashin cewa wannan hukunci ba zai hau kan Najeriya.

Ko ya abin zai karke? Dabara ta rage ga mai shiga rijiya!

Me hakan Zai haifar?

Ko tantama babu wannan hukunci idan ya tabbata zai jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki matuka. Domin ba a taba yi wa wata kasa irin wannan hukuncin biyan diyyar karya yarjejeniyar kwangila ta makudan kudade haka kamar Najeriya ba.

Share.

game da Author