Hukumar ’Yan Sanda ta kara ruruta caccakar da dimbin jama’a ke wa sojoji, dangane da kisan zaratan ‘yan sandan da ke farautar masu garkuwa da mutane, cewa babu wata hujjar da za su fito su shaida wa duniya cewa ita ce ta sa suka kashe ‘yan sanda uku a Jihar Taraba.
A yau Alhamis ne ‘yan sanda suka maida wa sojoji kakkausan martani, bayan da hukumar tsaro ta sojoji ta bayyana cewa ta harbe ‘yan sandan a ranar Talata, a bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.
Sojoji sun harbe ‘yan sandan bayan sun kamo wani rikakken dan fashi da kuma garkuwa da mutane, sun sa masa ankwa, a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Jalingo da shi.
‘Yan sanda sun zargi sojoji da cewa da gangan suka harbe jami’an na su, domin bayan sun kashe su, sai kuma suka saki wanda aka kamo din, ya gudu.
Sun kuma garkama wa sojoji zafafan tambayoyi guda takwas, dangane da kisan zaratan na su da suka bayyana cewa shahararrru ne wajen kamo manyan masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
Ciki harda tambayar cewa ” Idan Sojojin da gaske suke su fadi yadda suka yi da gogarman masu garkuwa Alhaji Hamisu dake tare da ‘yan sanda a lokacin da suka bude musu wuta? An ce da dagangar suka kwato shi suka kwance masa ankwa sannan suka sake shi ya gudu abinsa bayan sun kashe ‘yan sandan.
Wadannan zaratan ‘Yan sanda na daga cikin wadanda suka ceto Magajin Garin Daura a hannun masu garkuwa a dajin Kano, sannan suna daga cikin wadanda suka kamo wasu gaggan shugabannin Boko Haram.
Su dai wadannan ‘Yan sanda da sojoji suna daga cikin wadanda suma kamo wannan hatsabibin mai garkuwa da mutane ana biyan miliyoyin kudin fansa, Evans.
‘Yan Najeriya da dama da suka tofa albarkacin bakunan su kan wannan kisa da sojoji suka yi sun yi tir da aikata haka sannan sunce ya zama dole abi wa iyalan wadannan zaratan ‘Yan sanda hakkinsu sannan a hukunta sojojin da suka aikata wannan mummunan aiki.
‘Yan sandan da suka ras rayukan su sun hada da
Insfekta Mark Ediale, dan asalin jihar Edo, Sajen Usman Dan’azumi da Sajen Dahiru Musa, duk ‘yan asalin Jihar Taraba ne.
Discussion about this post