Sai da muka biya diyyar naira Miliyan 5.5 kafin masu garkuwa suka saki ‘ya’yan mu – Iyaye

0

Bayan shirga wa ‘yan Najeriya Karya da rundunar ‘yan sanda suka yi cewa sun ceto daliban jami’ar Ahmadu Bello da masu garkuwa suka yi dasu ranar Litinin ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwan dasu sun karyata ‘yan sandan inda suka ce sai da suka biya diyyar naira miliyan 5.5 kafin masu garkuwan suka sake su.

Idan ba a manta ba kakakin rundunar ‘yansanda jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya sanar jiya cikin dare cewa zaratan ‘yan sanda sun ceto uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Shima mai taimakawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai Bashir Ahmad ya tabbatar da haka inda har ya tada a shafin sa na Tiwita.

Jim kadan bayan Bashir ya rubuta haka sai ‘yan Najeriya suka yi masa caa, inda suka karyata wannan rubuta na sa suna masu cewa ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwa da suka biya kudin diyya kafin aka saki ‘yan uwan su.

Daga baya Bashir ya roki ‘yan Najeriya bisa wannan rubutu da yayi cewa yayi amfani da sanarwan da ‘yan sanda suka fitar ne.

‘Yan uwan wadannan dalibai sun ce tun bayan sace ‘yan uwansu da akayi suka rika yin waya da masu garkuwan har Allah yasa suka kai ga amincewa za su karbi naira miliyan 5.5 akan dalibai uku. Daga nan ne suka amince suka sake su.

Har yanzu uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su na tsare a hannun masu garkuwan.

Share.

game da Author