Bankin Duniya (World Bank), ya fallasa sunayen wasu manyan kamfanonin gine-gine na kasar Chana shida cewa an same su da laifin harkallar kwangiloli masu tarin yawa.
Bankin Duniya ya ce wsdannan kamfanoni da ke aikin a wurare daban-daban a Najeriya, sun karya ka’idojin ayyukan kwangilolin da ‘World Bank’ ya gindaya a fadin duniya. Kuma bankin ya nuna rashin jin dadin sa.
Kamfanonin da aka fallasa din sun hada da:
1. China Railway Construction (International) Nigeria Company Limited.
2. China Railway 18th Bureau Nigeria Ltd.
3. China Nageria Engineering Company Ltd.
4. CCECC Nigeria Lekki (FTA) Construction Ltd.
5. CCECC Railway Petroleum and Gas Company Ltd.
6. CCECC Nigeria Company Ltd.
Wadannan kamfanoni a yanzu su ne ke fsntamawa a Najeriya su na ayyukan kwangilolin gina hanyoyin jiragen kasa, titinan gwamnatin tarayya da na jihohi, gina rukunin gidaje na gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi, gina filayen saukar jirage da ma harkokin man fetur da wasun su ke yi.
Bankin Duniya ya haramta su daga cikin kamfanonin da ya amince a bai wa duk wata kwangilar da ta shafi harkar kudaden da aka ramto ne daga Bankin Duniya ko kwangilar bankin, har tsawon shekara daya. Wato daga Yunin 2019 zuwa Yulin 2020, 3 Ga wata.
Bankin Duniya ya ce wadannan kamfanoni sun rika karya ka’idojin da bankin ya shimfida wajen gudanar da kwangiloli ba tare da nuku-nuku ba, ko harkalla ko rufa-rufa ba.
Bankin ya ce an rika gudanar da wasu kwangilolin ba tare da tartibin cikakken bayanin yadda aka kashe kudaden da hujjar abin da aka yi da kudaden ba.
Takardar nuna bacin rai da Bankin Duniya ya fitar a cikin shafin sa na Intanet duk ya bayyana wannan bayani.
Sai dai kuma bai fayyace dalla-dalla adadin kudaden da kamfanonin suka yi wa sabt-ta-juyat-ta ba. Amma dai ya ce sun karya ka’idar dokar da bankin ya shimfida ta 1.16(a)(ii).
Kamfanin China Railways dai shi ne ke aikin titin jirgin kasar nan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna. Ya na daga cikin katafariyar kwangilar dala bilyan 18, wato kwatankwacin naira tiriliyan 2 na aikin kwangilolin hanyoyin jirgin kasa a fadin kasar nan.