Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce babu wani abin damuwa dangane da rashin amincewar da Kotun Koli ta yi, inda kotun ta hana PDP duba rumbun ajiyar sakamakon zaben da ita PDP ta yi ikirarin cewa INEC na da shi.
Atiku ya yi wannan bayani ne ta bakin babban lauyan sa, Eyitayo Jegede SAN, bayan da Kotun Koli ta yanke hukuncin hana a binciki rumbun ajiyar alkaluman zabe, wato ‘server’, jiya Talata.
Atiku ya ce tuni dama sun hango yadda hukuncin kotun zai kasance, ba za bari su duba rumbun ajiyar na intanet ba. Don haka tun lokacin da ake tabka mahawara a kotu, kafin ranar yanke hukunci, sun rigaya sun dauki wani matakin da ya kamata su dauka, a matsayin su na wadanda suka shigar da kara.
“Kada a damu, babu wani abin damuwa dangane dahukuncin da Kotun Koli ta yanke.”Inji Atiku, ta bakin Babban Lauya Jegede.
“Batun ‘server’ dama dai kokari ne domin a tabbatar da cewa an yi wa PDP magudi a zaben 2019 yayin tattara sakamakon zabe.
“Don haka da muka fahici kotu ba amincewa za ta yi mu shiga shikin rumbun domin mu yi bincike ba, sai muka gabatar da shaidun bayyanannu a kotu, na kwafe-kwafen takardun sakamakon zabe na gidogar da aka shirga a lokacin tattara sakamako domin tantancewa.”
Atiku ya ce ya na da yakinin cewa Kotun Sauraren Kararakin Zaben Shugaban Kasa za ta yi masa adalci a ranar da za ta yanke hukuncin karar da ya shigar.
Atiku ya je Kotun Koli ne inda ya nemi ta tilasta wa Kotun Daukaka Kara amince masa shi da PDP su shiga rumbun tara alkaluman zaben INEC su yi binciken fito da shaidar yadda aka tattara sakamakon zabe a cikin rumbun na intanet.
Sai dai kuma Kotun Koli ta ki amincewa, a bisa dalilin cewa har yanzu batun ya na Kotun gaban Kotun Daukaka Kara.