RIGAKAFI: Akwai babban aiki a gaban Najeriya – EU

0

Tarayyar Kasashen Turai (EU) ta bayyana cewa har yanzu fa akwai sauran aiki a gaban mahukuntan Najeriya musamman game da aikin yin rigakafi a kasar.

EU ta fadi haka ne a taron tantance yadda Najeriya ke kashe kudaden tallafi da take samu daga kungiyoyin kasashen.

Jakadan EU a Najeriya da yammacin Afrika Ketil Karlsen yace shekaru 17 da suka gabata kenan EU tana tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya musamman domin inganta kiwon lafiyar yara kanana ta hanyar yi musu rigakafi.

Ya ce a lissafe EU ta tallafa wa Najeriya da Euro miliya 200 a tsakanin wadannan shekaru amma duk da haka adadin yawan yaran dake mutuwa a kasar baya misaltuwa.

A binciken da kungiyar kiwon lafiya (WHO) ta yi a Najeriya, sakamakon ya nuna cewa a duk shekara Najeriya na rasa akalla yara kanana miliyan daya a dalilin wani ciwo ko rashin lafiya.

A dalilin haka Karlsen yace EU ta daura damarar ci gaba da tallafa wa Najeriya.

Bayan haka shugaban kungiyar kula da yi wa yara allurar rigakafi na na hukumar WHO, Fiona Barka ta yabawa irin tallafin da EU ta rika ba Najeriya a tsawon wadannan shekaru har zuwa yanzu domin inganta kiwon lafiyar mutanen kasar musamman wajen kawar da cutar shan-inna.

“A yanzu haka Najeriya ta kusa yin shekaru uku cif ba tare da shan inna ya bullo ba wanda hakan na da nasaba ne da irin goyan bayan da EU ta rika ba kasar da sauran kungiyoyi.

“Tallafin ya taimaka mana wajen wayar da kan mutane sanin mahimmancin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi.

A karshe darektan hana yaduwar cututtuka da yi wa yara allurar rigakafi na hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na kasa (NPHACDA) Joseph Oteri ya yaba wa wannan tallafi yana mai cewa a dalilin samun wannan tallafin cibiyoyin kiwon lafiya dake karkara sun samu na’urar adana magungunan rigakafi dake amfani da hasken rana batare da an samu matsala.

Ya ce samun wannan na’ura ya taimaka wajen inganta yi wa yara kanana allurar rigakafi a musamman kauyuka da karkara.

Share.

game da Author