RASHIN TSARO: Da ƴan gari ake ta’addanci a Yankin Kudu Maso Yamma – Taron Obasanjo da Fulani

0

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya gana da shugabannin Kungiyoyin Fulani dake yankin Kudu Maso Yamma.

Obasanjo ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa ya kira wannan ganawa shine domin a samo mafita ga hare-haren da garkuwa da mutane da ya addabi mutanen wannan yankin.

A taron Obasanjo ya roƙi Fuƙani da su da taimaka wa mutanen yankin wajen ganin ankawo karshen matsalar garkuwa da mutane da yake neman zama ruwan dare a yankin.

Jogoran tawagar Fulanin Saleh Bayari tare da shugabannin ƙungiyoyin Fulanin yankin hadi da na jihar Kogi ya bayyana cewa wannan ganawa yana da matukar tasiri da alfanu.

” Babu inda wani zai tafi ko kuma ace wai ya bar wani yanki a kasar nan. Sai dai kuma dukkan mu a nan mun dan abin da ke faruwa a yanzu na rashin tsaro. Dole mu haɗa kai domin ci gaban yankin.

Kungiyar Gan Allah Fulani sun godewa Obasanjo bisa wannan gayyata da yayi musu.

” Wannan gayyata yana da matuƙar mahimmanci a gare mu sannan kuma ina so in sanar muku cewa duk da dangant yawa-yawan garkuwa da mutane da ake yi ga Fulani makiyaya, ina so in tabbatar muku cewa wannan ayyukan ta’addanci harda ƴan gari ake yi da haɗa baki a mafi yawan lokutta.

” Kamar yadda akwai batagari a cikin mu Fulani haka akwai bata gari a cikin ƴan gari wanda suke aikata ta’addanci a boye sannan kuma arika ƙala mana Fulani.

Share.

game da Author