RANAR MATASA: Gyara tarbiyyar matasa shine mafita ga kiwon lafiyar su – Kwararru

0

Tun a 1999 gwamnatocin duniya suka kebe ranar 12 ga watan Agusta a matsayin ranar matasa ta duniya domi yin tuni game da ingancin da ke tattare da gyara tarbiyyar matasan duniya.

A taron na bana wanda kungiyar ‘Africa Youth and Adolescent Network on Population and Development (AfriYAN) ta shirya a shafinta na tiwita ya yi kokarin tattauna matsalolin da ka iya bullowa a dalilin rashin wayar da kan matasa game da jima’I, haihuwa da amfani da dabarun dada tazarar iyali.

Kwararrun ma’aikatan ilimin da suka tofa albarkacin bakunan su a shafin sun bayyana cewa rashin yin haka zai sai sa a rika samun matsala daga matasan.

Kwararrun da suka tattauna a wannan hira sun hada da jami’ar kungiyar ‘Nigeria Health Watch’ Margaret Bolaji, Priscilla Usiobaifo mashawarciyar al’amuran matasa na kungiyar John Hopkins kuma shugaban kungiyar ‘Brave Heart Initiative (BHI) da Omowumi Ogunrotimi shugaban kungiyar ‘Gender Mobile’.

Matsaloli

Kwararrun sun nuna damuwarsu game da yadda rashin sani a harkokin da suka shafi saduwa na mace da Namiji, haihuwa da amfani da dabaraun bada tazaran iyali ya zama matsalola matuka a zamantakewar mutane.

A yanzu haka mafi yawan iyaye basu koyar da ya’yan su harkokin jima’i wanda hakan kan sa a rika samun ya’ya na fandarewa ana lalata da juna a koda yaushe har ta yadda bai kamata ba.

Haka kuma ko a makarntun mu na Boko ba a daukan lokaci domin karantar da yara ire-iren haka domin ci gaban su.

A Najeriya bincike ya nuna cewa kashi 43.5 bisa 100 na ‘yan mata masu shekaru 15 zuwa 19 suna da masaniya game da harkokin jima’a da saduwa da juna.

Mafita

Margaret Bolaji ta yi kira ga gwamnati kan maida hankali wajen wayar da matasa wajen hanyoyin saduwa da juna da yadda za a iya kiyaye wa.

Bolaji ta ce yin haka ya hada da kirkiro darussa da zai rika wayar da kan mutane musamman matasa game da hakan. Sannan a kula kada a kauce wa karantarwar addina da al’adxu domin kada garin neman kiba kuma a samo rama.

Share.

game da Author