RAHOTON MUSAMMAN: Yadda Sojoji suka kashe Ƴan sanda uku da gangar suka saki Hamisu

0

Idan dai ba a manta ba a cikin makon da ya gabata ne wasu sojoji dake aiki a hanyar Ibi zuwa Wukari suka bindige wasu zaratan ‘ƴan sanda uku a hanyarsu na zuwa Jaligo tare da wani gogarman masu garkuwa da mutane da suka kamo.

Su dai waɗannan ‘yan sanda ana ji da su matuƙa a ƙasarnan sannan suna daga cikin waɗanda suka kamo ƙasurgumin mai garkuwa da mutane nan mai suna Evans, sannan suna daga cikin zaratan ‘ƴan sandan da suka ceto Magajin Garin Daura daga hannun masu garkuwa da mutane.

A dalilin wannan kisa da aka yi wa waɗannan ‘ƴan sanda ne yasa PREMIUM TIMES ta yi tattaki har zuwa garin Ibi da Wukari domin gani da ji wa ƙanta ainihin abinda ya faru a wannan lokaci.

Isar wakilin mu garin Ibi ke da wuya sai ya garzaya kai tsaye zuwa garin Gidindawa inda nan ne mazaunin Alhaji Hamisu Wadume da ‘ƴan sandan suka ƙai wa farmaki kuma suka kamo.

Kusan duk waɗanda suka tattauna da wakilin mu a garin sun ba da bayanai iri ɗaya ne.

” Ko da ƴan sandan suka iso garin Gindinwaya sai mutanen garin suka fafuri farar bas ɗin da aka saka shi Hamisu a ciki. Bayan sun isa shingen sojoji na farko ne sai suka sanar wa sojojin dake wannan wuri cewa ga wasu masu garkuwa da mutane can sun yi garkuwa da wani Alhaji Hamisu.

” Da jin haka sai suka yi wa sojojin dake shinge na gaba waya cewa su tare ga wani mota nan zuwa, masu garkuwa ne a ciki.

Ko da suka iso wannan wuri sai kawai suka buɗewa motar wuta babu ƙaƙƙautawa.

Haka nan motar ta kife sannan ‘ƴan sanda biyu suka mutu nan take. Ɗaya daga cikin ƴan sandan da bai mutu ba ƴa nemi ya nuna musu shaidar shi ɗan sanɗa ne amma suka ki sauraren sa suka ƙarisa shi abinsu.

Wani da ke wannan wuri ya shaida wa wanda muka tattauna da su cewa bayan sun ƙarisa wannan ɗan sanɗa sai suka kwabe ankwan dake maƙale a hannun Hamisu aka saka shi a cikin wata baƙar mota aka tafi da shi can garin Gidindawa.

Toh bayan sun tafi sannan kuma sojoji suka fara jin cewa lallai sun tafka ɓarna sai suka koma can garin Gidindawa domin kamo Hamisu amma inaa, tuni ance ya waske ta ruwa a wani kwale-kwale ya bar garin.

Baya ga haka an gano cewa akwai wani babban soja da ya taka rawar gani wajen ganin an kubutar da Hamisu daga hannun ‘yan sandan da suka cafke shi.

Wannan soja mai muƙamin kaftin ance ya yi matukar sabawa da Hamisu kuma yana morar sa sosai domin shine ma ya kwashe bindigogin ƴan sandan da sojojin suka kashe ya tafi da su.

” Shi fa Alhaji Hamisu yana da farin jini matuƙa. Yana ɓarin kuɗi yadda kasan gwamnati ce kanta. Wannan abu fa har da sarakuna masu faɗa aji suna amfana da wannan mutum. Shi kansa Kaftin Usman yana da masaniya akai domin yana moran sa kuma yana amfana da shi. Shi ya kwashe bindigogin ƴan sandan da sojoji suka kashe yayi awon gaba da su.

Ba da gangar sojoji suka kashe ‘ƴan sanda ba

Idan ba a manta ba a wani abin tashin hankali da ban tsoro da ya auku a hanyar Ibi zuwa Jalingo, dake jihar Taraba ranar Laraba shine yadda gungun sojoji suka yi wa tawagar ‘yan sandan kwantar bauna suka kashe ‘yan sanda uku.

Kakakin rundunar ‘Yan sanda Frank Mba ya bayyana haka a takarda da ya fitar ranar Laraba cewa sojojin sun budewa ‘yan sandan wuta ne bayan sun kamo wani gogarman masu garkuwa da aka dade ana farautar sa mai suna Alhaji Hamisu.

Frank yace Hamisu yayi kaurin suna a wannan yanki wajen yin garkuwa da mutane.

‘Yan sandan sun farwa maboyar sa ne inda suka kamo shi zasu kai shi garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

” Jami’an ‘yan sandan sun isa shingen sojojin ne inda da ganin su sai suka bude musu wuta duk da sun gane cewa ‘Yan sanda ne ke tahowa. Bayan sun kashe uku daga ciki sai suka saki Alhaji Hamisu a wannan daji.

Sai dai kuma Kakakin rundunar Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya bayyana cewa ba da gangar bane sojojin suka budewa yan sanda wuta ba.

Abinda ya faru shine, Sojoji sun bi wannan mota da ke dauke da wasu masu garkuwa da mutane bayan wasu kauyawa sun yi waya cewa wasu sun yi garkuwa da Alhaji Hamisu, gogarman masu garkuwa a wannan yanki. Sau uku sojoji na kokarin tsayar da wannan mota kirar Bas fara amma suna kin tsayawa.

” Bayan haka ne sojoji suka bi motar a baya suka bude mata wuta. Sai bayan motar ta tsaya ne sannan suka gane cewa akwai ‘yan sanda a ciki.

Sagir yace an kashe masu garkuwa 4 sannan wasu sun samu rauni a jikin su.

Tambayoyi 15 da ‘Yan sanda ke neman amsar su wajen Sojoji dake musanta kisan da suka yi

Tambaya ta farko kuma mai muhimmanci it ace, shin ina Alhaji Hamisu Bala Wadume, miloniyan mai garkuwa da mutane wanda ‘yan sanda suka kama, suka sa masa ankwa?

Idan shi ne sojoji ke zaton an sato shi har suka je ceton sa, to ya aka yi suka same shi da ankwa?

Me ya sa ba za su yi bincike ba sai kawai su kwance masa ankwa su sake shi?

Wane ne ya kira su ya shaida musu cewa masu garkuwa sun saci wani sun gudu da shi, alhali kuwa ‘yan sanda ne suka kama mai garkuwa suka saka masa ankwa?

Me ya sa ba su kama wanda suka wai shi ne ya kira sojoji ya ce musu ga shi can an yi garkuwa wa wani ba.

Kuma wane mutum ne aka fada wa sojojin cewa an yi garkuwa da shi, alhali su ‘yan sanda mai garkuwa da mutane suka kamo?

Karya ne da aka ce wai ‘yan sanda ba su bayyana musu cewa su jami’an tsaro ba ne. domin bidiyon da ake watsawa a soshiyal midiya ma za a ji har wani soja na fada da karfi cewa ‘yan sandan daga Hedikwatar Abuja suke.

Ba gaskiya ba ne da aka ce hukumar ‘yan sanda ba ta sanar da jami’an ta daga Abuja za su ce Taraba kamo mai garkuwa da mutane ba. Sun je hedikwatar ‘yan sanda ta Jalingo sun kai rahoto, kuma sun je Ofishin Shiyya na Wukari sun kai rahoton cewa an turo su Taraba su yi kame. Hatta jami’an CID na Taraba ma da su aka je kamen.

Hukumar ‘Yan Sanda a Abuja ta bayyana bayanin da sojojin Bataliya ta 93 da ke Takum suka yi da suka ce sun dauka masu garkuwa ne, cewa rashin mutunci ne da kuma rashin kyautawa karara.

Share.

game da Author