Kamfanin Man Fetur na NNPC, ya bayyana dalilin tashin farashin man fetur, cewa hakan ya faru ne saboda matsin-lambar yawan bukatar sayen sa daga masu sayarwa.
Kakakin NNPC, Ndu Ughamadu ne ya bayyana wa manema labarai haka a jiya Lahadi a Abuja cewa sayar da kananzir a tsarin ta-ci-barkatai ne ya haifar da Karin farashin can tsakanin mai saye da mai sayarwa.
“Saboda kananzir ba shi da tsauraran matakan sa-ido na ka’idar sayar da shi ne kamar yadda ake yi wa fetur, shi ya sa kudin kananzir ya karu, wata rana kuma a ga ya yi kasa.” Inji shi.
“Abin da ake fuskanta a yanzu shi ne kara yawan bukatar sayen kananzir da ake yi ce ke kara sa ya na kara tsaida a hannun masu sayarwa.
Binciken da aka yi ya nuna cewa gidajen mai da ke wajen Birnin Tarayya, Abuja ya nuna cewa ana sayar da litar kananzir daya a kan naira 400 har zuwa 500.
Wasu gidajen mai a Dutsen-Alhaji, Kubwa da Zuba duk ba su sayar da kananzir a lokacin da wakilin mu ya je can.
Akasarin masu amfani da kananzir duk a hannun ‘yan gada-gada ko ‘yan bumburutun cikin unguwanni ko gefen titina a hannun ‘yan tireda.
Ndamadu ya yi alwashin cewa NNPC zai ci gaba da wadatar wa kasar nan man fetur da kuma kananzir.
Ya ce Karin kudin kananzir ba daga NPC ba ne, daga masu sayarwa ga masu amfani da shi a gida ne.
Discussion about this post