Najeriya za ta hukunta masu hannu a neman janyo mata asarar naira Tiriliyan 3.2

0

Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta hukunta jami’an ta da ke da hannu wajen yin sakacin da har ya kai Kotun Hukunta Masu Karya Yarjejeniyar Kwangila ta Landan ta kakaba wa kasar biyar diyyar dala bilyan 9.

Dala bilyan 9 dai na kwatankwacin naira tiriliyan 3.2 ne. Malami ya yi wannan bayani jiya Alhamis, yayin da ya sake kama aiki a matsayin ministan shari’a, zango na biyu.

Malami ya zargi gwamnatin Jonathan da “hada baki da wasu ‘yan kakudubar kasashen waje da kokarin karya tatalin arzikin Najeriya da kuma karya arzikin al’ummar Najeriya.”

Ya ce matsayin su na gwamnati, ba za su zuba ido su kyale wadanda ke da hannu wajen kokarin jawo wa Najeriya wannan dimbin asarar da ba ta misaltuwa ba.

“Duk wani mai hannu kai-tsaye ko a fakaice wajen nemowa, samowa, sa hannu da kuma amincewa da wanan yarjejenya sai an hukunta shi.” Inji Malami.

PREMIUM TIMES HAUSA dai a ranar Alhamis ta buga cikakken rahoto na musamman wanda ta nuna “Sakacin gwamnatin ‘Yar’Adua, Jonathan da ta Buhari wajen neman janyo wa Najeriya asarar naira tiriliyan 3.2.”

Najeriya na neman tabka wannan asara ce a matsayin hukuncin biyan diyyar da kotun Ingila ta ce ta yi wa kamfanin P&ID, sakamakon karya jarjeniyar kwangilar da aka zargi Najeriya ta yi.

An rattaba wannan kwangila ce tun cikin 2010, lokacin da tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru ’Yar’Adua ke kwance Asibitin Saudiyya ya na jiyya.

Ministan Harkokin Man Fetur na lokacin, Rilwanu Lukman ne ya sa wa kwangilar hannu. Lukman dai ya rasu tun cikin 2014.

Masu sharhi dai tun a lokacin sun rika mamakin yadda aka sa hannun amincewa da kwangilar a lokacin da Umaru Yar’Adua ke asibiti.

An yi zargin cewa wasu ‘yan ba-ni-na-iya sun karbe sha’anin mulki a lokacin, suka wancakalar da matsaimakin Umaru na lokacin, wato Goodluck Jonathan.

Minista Malami ya ce gwamnatin Najeriya za ta kare kan ta a kotu, tare da tabbatar da cewa ba ta biya diyyar ba.

Har ila yau, Malami ya bayyana hukuncin a matsayin wani abin takaici, kuma sakamako ne na wata harkalla da wasu marasa kishin kasar nan suka yi a zamanin gwamnatin baya.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya tare da hadin kan EFCC za su ci gaba da binciken wadanda ke da hannu wajen harkallar amincewa da sa hannu a kwangilar, wadda ke neman janyo wa kasar nan mummunar asarar da wata kasa a duniya ba ta taba yin irin ta ba, ta hanyar hukuncin biyar diyyar karya yarjejeniyar kwangila tsakanin wata kasa da wani kamfani na wata kasa.

Sai dai kuma ana ganin wannan magana da Malami ke yi, ba za ta yi tasiri ba, ganin cewa tuni gwamnatin Buhari ta san da wannan batun. Sannan kuma ta san da cewa Rilwanu Lukman da ya sa wa kwangilar hannu ya mutu tun cikin 2014.

Sannan kuma gwamnatin Buhari ba ta da tarihin hukunta wadanda suka yi barnar janyo wa kasar nan mummunar asara.

Idan ba a manta ba. Gwamnatin Buhari ta biya tsoffin ma’aikatan kamfanin jiragen saman Najeriya, wato Nigeria Aiways diyyar bilyoyin nairori.

Sai dai kuma abin mamaki shi ne, yadda har yau gwamnatin Buhari ba ta hukunta wadanda suka durkusar da Nigeria Airways ba.

Hasali ma, hudu daga cikin fitattun mutane 10 da suka durkusar da Nigeria Airways, duk su na cin moriyar gwamnatin Buhari a yanzu haka.

Share.

game da Author