Najeriya na gab da yin sallama kwata-kwata da cutar Shan-inna – WHO

0

Kungiyoyin kiwon lafiya na ciki da wajen kasar nan sun gudanar da taro a Abuja a wannan mako domin yi wa hukumomin dake da hakkin kawo karshen cutar Inna a kasar da su maida hankali domin ganin an yi sallama da cutar kwata-kwata.

Najeriya, Afghanistan da Pakistan na daga cikin kasashen duniyan da suke fama da cutar a duniya.

Yi wa yara kanana allurar rigakafi kafin su kamu da cutar, tsaftace muhalli na daga cikin hanyoyin dake hana sa a kamu da cutar.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakon farko na Najeriya (NPHCDA) Faisal Shu’aib ya bayyana cewa Najeriya ta maida hankali matuka domin ganin t karbi shaidar yin sallama daga cutar kwata-kwata a kasar.

Shu’aib ya ce ana ba kasar da ta yi akalla shekaru uku basu samu rahoton bullowar cutar a ko ina ba. Daga nan sai a mika mata shaidar rabuwa da cutar kwata-kwata.

A karshe wakiliyar asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Pernille Ironside ta yaba wa himman da Najeriya ta rika yi a tsawon shekaru uku da suka wuce domin ganin ta yi sallama da cutar.

Share.

game da Author