Na kashe wa harkokin ilmi naira tiriliyan 1.3 daga 2015 zuwa yau – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kashe kusan naira tiriliyan 1.3 wajen inganta harkokin ilmi, tun daga 2015 zuwa yau.

Buhari ya bayyana haka yau Alhamis a lokacin da ya ke kaddamar Cibiyar Ilmin Difloma Mai Zurfi, wadda Babban Bankin Najeriya, CBN ya gina a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Wata sanarwa da Kakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya yi amfani da lokacin ya kara jaddada kokarin da wannan gwamnati ke yi wajen ganin ta samar da ingantaccen ilmi ga ‘yan Najeriya, duk kuwa da karancin kudin da gwamnatin sa ke fama da su.

Da ya ke jinjina wa CBN bisa kokarin san a gina cibiyar a ABU, Buhari ya ce cibiyar za ta kara bijiro da kyawawan ayyukan hangen-nesan da marigayi Sardauna Ahmadu Bello ya samar har ta kai ga ya kafa jami’ar shekaru 60 da suka gabata.

Ya kara tunatar da irin gudummawar da Jami’ar ABU ta bayar wajen ci gaban kasar nan baki daya. Ya ce wannan tabbas ba sai taba sawa a manta gagarimar gudummawar da Sardauna ya bayar ba.

Daga nan sai Buhari ya yi alkawarin ci gaba da bai wa harkokin ilmi muhimmanci a dukkan matakan ilmin kasar nan.

Share.

game da Author